Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi
Cibiyar gudanarwa ta Sarki Salman na ƙasar Saudiyya, ta rarraba kayayyakin abinci ga gajiyayyu da ‘yan gudun hijira, 4,399 waɗanda ‘yan ta’adda suka kora daga garuruwansu, da ke Jihar Kebbi.
Abincin ya ƙunshi hatsi da shinkafa da taliya da tumatur na gwangwani da man-girki da kuma gishiri mai gina jiki.
A sa’ilin taron, darakta-janar ta hukumar bada agaji ta ƙasa, NEMA, Hajiya Zubaida Umar, ta bayyana cibiyar gudanarwa ta Sarki Salman, a matsayin ‘ginshiƙin jin-ƙai’ da ke aiki tare da Najeriya, wurin bayar da agaji ga gajiyayyu da waɗanda bala’oi suka rutsa da su.
Zubaida, wadda daraktan ayyuka na musamman na hukumar, Fatima Suleiman Qassim ta wakilta, ta jaddada cewar, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya jajirce wurin kawo ɗauki da kawar da duk wani ƙalubale daga jama’a gajiyayyu da kuma al’ummomin da musibobi ke addaba a Najeriya.
Da yake rabon kayayyakin abincin, Gwamnar Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana godiya ga Cibiyar Gudanarwa ta Sarki Salman na Saudiyya, dangane da yadda ta wanzar da nuna jin-ƙai da kawo gudunmawa ga al’ummar Jihar Kebbi.
Gwamnan ya yi tambihi ga waɗanda aka bai wa abincin, da kada su kuskura su kai su kasuwa su sayar, amma suyi amfani da su yadda ya dace tare da iyalansu.
