Ba mu amince da wasan kwaikwayon Gwamnatin Zamfara ba – Wasu ‘yan kishin Jihar

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Wasu masu fafutukar zaman lafiya da cigaban al’umma a Zamfara sun yi kira ga gwamnan Jihar, Dauda Lawal da ya daina siyasantar da mulkin ‘yan Jihar tare da mayar da hankali wajen ayyukan da ya alƙawuranta wa mutane.

Jaridar ‘Daily Post’ ta ruwaito cewa, ƙungiyar ta buƙaci gwamnan da ya bayyana wa al’ummar Jihar jadawalin nasarorinsa cikin shekara guda da yake kan karagar mulki.

A cikin satinnan ne shuwagabanni a matakai daban-daban kama daga kan shugaban ƙasa zuwa gwamnoni suka bayyana ire-iren nasarorin da suka samu a yayin da suke bikin cikar shekara ɗaya a kan kujerunsu, saɓanin gwamnan Zamfara ya fake da matsalolin tsaro dake addabar Jiharsa.

Sun ƙara da cewa madadin mayar da martani da sukan takwarorinsa da ma wasu hukumomi, kamata yayi ya fuskanci abubuwan da zasu inganta rayukan al’ummar Jihar da kuma daƙile matsalolin tsaro da take fama da shi tsawon lokaci.

Haka nan, sun ƙara da cewa, Dauda ya yi alƙawarin daƙile matsalolin tsaro cikin kwanaki 100 amma har yanzu ba’a cimma hakan ba inda suka bada misali na sabbin hare-haren da aka kai a yankunan Bilbis, Tsafe, Sakajiki, Faru, Dogon Kade, Kanwa, Ruwan Dawa, Malele, Mutunji da wasu wurare da dama ciki har da babban birnin Jihar, Gusau wanda suka ce bai je ba kuma bai aika sakonnin jajantawa ga mutanen ba.

Mutanen sun ƙara da cewa, a lokacin da aka yi garkuwa da ɗalibai a Jami’ar Tarayya ta Gusau, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya turo tawaga domin jajantawa lamarin ƙarƙashin ministan tsaro, Mohammed Badaru inda suka ce gwamnan baya ƙasar kuma bai tura wakilai ba domin tarbar tawagar.

Daga ƙarshe, sun yi kira a gare shi da ya mayar da hankali wajen gudanar da ayyukan bunƙasa rayukan al’ummar Jihar da samar da tsaro ta hanyar yin haɗaka da dukkan masu ruwa-da-tsaki domin cimma nasara a shugabancinsa.

By Babaji