A Jihar Neja:’Yan bindiga sun mamaye gonakin mutum 3,000

Spread the love

Sama da mutane 3,000 da suka rasa matsugunansu a garin Erena bayan sun tsere daga yankunansu a kwanakin baya sakamakon hare-haren ’yan bindiga a yankin ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja, inda a halin yanzu suke fuskantar annobar yunwa sakamakon ƙarancin abinci.
An gano cewa, ’yan gudun hijirar na fama da yunwa a Erena duk da cewa, suna da wadataccen abinci a gonakinsu da ke yankinsu, yankin da ’yan bindiga suka mamaye kuma suka tare su isa ga gonakin.
Blueprint Manhaja ta gano cewa, mutane uku da suka yi ƙoƙarin samun abinci ga iyalai masu fama da yunwa daga ƙauyensu na Lantan ranar Talata ba su dawo da ransu ba, saboda ‘yan bindiga sun kashe su.
Wani ɗan gudun hijira a sansanin Erena, Adamu Saidu, wanda ya yi magana akan lamarin, ya tabbatar da cewa, an kashe surukinsa a harin na baya-bayan nan, inda ya ƙara da cewa, “an harbe waɗanda aka kashen ne a hanyarsu ta kai wa iyalansu abinci.”
Ya ce, ’yan fashin dajin ba su da aniyar yin garkuwa da su, domin neman kuɗin fansa. Sun kwashe kayan abinci da yawa, sun ƙona ƙauyuka da kayan abinci.
Ya ce, “dukkan mutanen da suka rasa matsugunansu daga waɗannan al’ummomi a halin yanzu suna fuskantar matsalar ƙarancin abinci da sauran abubuwan da ba su da wani taimako daga ko’ina. Don haka ne waɗanda abin ya shafa suka yanke shawarar yin kasada wajen samun abinci daga gonakinsu. Abin takaici an harbe su akan hanyarsu.”
Ya lissafa ƙauyukan da aka kai harin a ranar Talata da suka haɗa da Lantan, Roro, Rumuchi da Makuba, inda aka lalata dukkan gidaje, kayan abinci da sauran kadarori.
Har yanzu da yake kokawa kan lamarin, Adamu ya ce, “muna nan a sansanin ba mu da abinci ga ’ya’yanmu, don haka suka yanke shawarar koma wa ƙauye, don samun abinci lokacin da aka tattara su aka kashe su. Duk da cewa, sun ba mu damar ɗaukar gawarwakinsu kuma mun yi jana’izarsu a jiya (Laraba). Amma kamar yadda nake magana da ku yanzu sun ƙona ƙauyuka uku.
“Sun ƙona dukkan kayayyakin abinci a waɗannan ƙauyukan da suka haɗa da shaguna. Sun gaya mana cewa duk wanda ya kuskura ya dawo waɗannan ƙauyuka za a kashe shi,” inji shi.
Ko da yake babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnati ko hukumomin tsaro a jihar kan wannan sabon hari, wani tsohon Shugaban ƙaramar Hukumar Shiroro da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana lamarin da cewa, yana ƙara ta’azzara fiye da da.
“’Yan ta’addan ba sa neman kuɗin fansa, sai dai kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba,” inji shi.
Ya ce, “Idan suka ga mutum sai su kashe shi. Ba su yin garkuwa da mutane da neman kuɗin fansa kamar da. Suna kashewa da ƙona ƙauyuka da kayan abinci. Halin da ake ciki yanzu ya yi muni matuƙa.”
Ya kuma yi tir da rashin jami’an tsaro a yankunan da lamarin ya ke shafa, inda kuma ya ƙara da cewa, baya ga al’ummar Erena, babu jami’in tsaro guda ɗaya a ko’ina a kusa da al’ummomin da ake kai wa hari.

By ukarofi