Rikicin Masarautar Kano ya caɓe bayan umarnin kotu da na ’yan sanda

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO

Daga dukkan yanayin babu alamun lalubo warware rikicin da ke addabar Masarautar Kano a nan kusa bisa la’akari yadda har yanzu kotu da jami’an tsaro ke cigaba da taka rawa a cikin lamarin.
A jiya Alhamis ne Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ƙarƙashin jagorancin Alƙali Muhammad Liman ta yanke hukuncin cewa, ta na da hurumin sauraron ƙarar da aka kai gabanta kan tuɓaɓɓen Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, tsigaggen Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babban ɗan Agundi, ke ƙalubalantar sauke su.
Jim kaɗan bayan hakan kuma, sai Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da soke fita bukukuwan Hawan Sallah a jihar cikin wata sanarwa wacce Kakakin Rundunar, Abdullahi Kiyawa, ya rattaɓa wa hannu.
Tun da fari dai, da ma an yi hasashen cewa, rundunar za ta hana hawan tun bayan da Alhaji Aminu Bayero ya gayyaci hakiman masarautar kuma ya nemi jami’an tsaro su ba shi kariya, don gudanar da hawan, duk da cewa, Gwamnatin Jihar Kano ta riga ta tuɓe shi. Masu hasashe na ganin cewa, ya nemi ya yi hawan ne, don jami’an tsaro su hana hawan bakiɗaya, saboda Gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta dafa wa sabon Sarkin Kano da ta naɗa, Muhammadu Sanusi II, wajen gudanar da hawan.
A yayin yanke nata hukuncin, Babbar Kotun Tarayya ta yarda cewa, ba ta da hurumin sauraron shari’un da suka shafi masarautu, amma ta na da hurumin sauraron shari’un da suka shafi haƙƙin ɗan adam, wanda shine Aminu Babba yake ƙara akai. Don haka ta saka yau Juma’a a matsayin ranar da za ta saurari shari’ar.
Yanzu dai an wayi gari a Kano ana dakon mataki na gaba da kotun za ta ɗauka a yayin zaman na yau, inda ake hasashen za a iya samun wani hukunci, wana zai iya sake baddala lamarin.
A ɓangaren Gwamnatin Jihar Kano kuwa har kawo kammala haɗa rahoton nan ba ta bayar da wata sanarwa game da hakan ba, amma majiya mai tushe ta tabbatar wa Blueprint Manhaja cewa, tuni lauyoyinta sun garzaya Kotun ɗaukaka ƙara, don ƙalubalantar hukuncin da Babbar Kotun Tarayyar ta yanke hurumi kan shari’ar, inda su ke neman Kotun ɗaukaka ƙarar ta jingine hukuncin Babbar Kotun da cigaba da shari’ar har sai ita ma ta yanke nata hukuncin.

By ukarofi