Har aikin noma na yi don koyon aiki a Kannywood – Maskwani

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU

Muhammad Abdullahi Uzairu, wanda aka fi sani da Sanin Inna Maskwani, ķwararren mai kula da sautin fim (Saund Engineer) ne a Masana’antar Kannywood. A tattaunawarsa da Wakilin Blueprint Manhaja, IBRAHIM HAMISU, a Kano, za ku ji yadda yake gudanar da aikinsa a cikin shekaru 13 da ya yi a masana’antar fim. Ku biyo mu:

MANHAJA: Za mu so ka gabatar mana da kanka ga masu karatun mu.
MASKWANI: Sunana Muhammad Abdullahi Uzairu wanda akafi sani da Sanin Inna maskwani.

MANHAJA Ko za ka bamu taƙaitaccen tarihinka?
MASKWANI Ni ɗan Kano ne anan aka haife ni anan nake rayuwata, sannan a nan na yi karatuna, na yi makaranta allo ta malam Ibrahim Bakin Ruwa daga bisani na dawo na shiga Makarantar Jakara Special primary school.
Na yi karatun junior secondary school a Abubakar Saddiq nan jikin gidan mai bargo Kwalwa Shehe. Na dawo nai senior secondary school Shahuci.

Ta yaya ka samu kanka a masaantar Kannywood?
Ta hannun wani bawan Allah mai suna Habibu Sani, mun hadu da shi akan yadda za mu rinƙa yin gajerun finafinan akan Fiqhu da Tauhidi don amfanin al’umma. Wanda har yanzu muna nan akan haka.

A lokacin da ka shigo Kannywood da mai ka fara?
A lokacin da na shigo Kannywood na fara da koyon ‘Camera da Light’ da ‘makeup’ daga bisani na koma koyan ‘editing’ da ‘sound’ a tare.

A wacce shekara kenan?
A shekarar tsakanin 2011 zuwa 2012 na fara.

Mene ne takamaiman aikin ka a cikin fim?
Ɗaukar Sauti wato ‘Sound Engineer’.

Da me da me ake buƙata idan za a yi aikin ɗaukar sauti a fim?
A jimlace abubuwan da ake buqata su ne: Na’urar daidaitawa da ɗaukar sauti (Zoom Recorder), Boom Mic. Doguwar sandar maƙala Zoom Mic, Kwanson Soson hana shigar Iska yayin ɗaukar magana da kuma Radio Mic, sai kuma wayar da ke haɗa mic da zoom.

Wani sai ya ce kamar kunyi ƙaranci a masana’antar Kannywood, shin haka ne?
A’a, ana ganin kamar haka, saboda wasu ‘producers’ ɗin sun fi so su fita aiki da mai ɗaukar sauti wane kuma dalilin iya ɗaukar sautin su; don haka ba kowanne mai ɗaukar sauti hankulansu ke kwantawa da su ba in zasu fita aiki. Amma muna da yawa domin duk inda ake ɗaukar shirin fim dole a samu masu ɗaukar sauti (Sound recorder ).

Daga lokacin da ka fara zuwa yanzu waɗanne irin nasarori ka samu?
Koyawa wasu aikin ɗaukar sauti, kuma suna nan suna gudanar da ayyukansu babu wata matsala a cikin masana’antar. Alhamdulillah.

Waɗanne irin ƙalubale kake fuskanta a Kannywood?
Akwai ƙarancin kayan aiki, musamman na zamani da ake amfani da su a duniya, da kuma abubuwan da ya dace a rinka biyan mu Sound Engineer. Shi mai aiki Sound Engineer ba ya hutawa tun daga farkon ɗaukar fim har ƙarshe, idan ana aiki. Shi ne a tsaye ko durƙushe ko zaune yana kula da shigar sauti a tsaftace ba wata matsala, da kuma riƙe sandar abin ɗaukar maganar. Domin duk kyan hoto idan babu sauti mai kyau, an yi aikin wofi sai an sake ɗauka, wannan ne ya sa a harkar fim da media sauti da hoto ake ɗaukarsu da muhimmancin gaske.

Wane ne maigidanka a Kannywood?
Sunanan da dama; amma babu kamar shi Habibu Sani. Mutum ne da ya bani shawarwari da suka taimakawa rayuwata. Bani kadai ba ma, Habibu Sani ya reni mutane da dama waɗanda suka yi fice a masana’antar. Wallahi ko yanzu ka je wajen sa zai kare ka da wasu abubuwan game da shirin fim, radiyo da kuma TV. Sannan ba ya gajiyawa shiyasa na ɗauke shi a matsayin uba. Sai dai in ce Allah ya saka masa da alheri.

Ko za ka iya tuna wani aiki da ya baka wahala wajen yin sa?
Gaskiya akwai su da yawa, akwai wani fim saboda tsabar wuya ƙarfe uku na dare na taho Kano da ga Abuja, akwai wani aikin da muka je daga kwanar Dawaki na fara tafiya a ƙafa ga ruwa na dukana ga dare har sabon titin ɗorayi, saboda an tashi na fito ba daɗewa kowa ya tafi ruwan sama ya tsuge na fake, na ga 1 na dare ta kawo kai, haka na taho har sabon titi ruwa na duka na.

Wane aiki ne kake alfahari da shi wajen aikinsa saboda ka yi abinda ya kamata?
Suna da yawa wasu ma na manta sunan su, amman na kusa-kusa sun haɗa da: ‘Uku Sau Uku’, ‘Anti Daba’, ‘Mizani’ ‘Buri’, ‘Bilkisu’ Tv series, ‘Lulu da Andalu’ Sabon Salo, ‘Kalma Daya’, ‘Zaluma’, ‘Ruwan Dare’ radiyo drama.

Mene ne burinka a nan gaba?
Burina shi ne masana’antar shirin fim ta Hausa ta tsaya da ƙafafunta. Sannan mu ƙaunaci juna da kula da haƙƙin juna, to insha Allah albarkar da darajar sana’ar ta fim za ta dawo a cigaba da harkar arziki. Babu abinda muka rasa a Kannywood face kuɗaɗen da za su rinƙa juya al’amura.

Wacce shawara za ka bai wa mai sha’awar shiga aikin ka na ɗaukar sauti?
Shawara ita ce na farko sai an samu sha’awar aikin a zuci, sai nutsuwa, jajircewa gami da yin hakuri wajen koyon aikin da kuma rakawa da addu’a. Duk wanda ya rungumi waɗannan abubuwa zai yi nasara akan komai a rayuwarsa. Domin ni ɗin nan har aikin noma na yi akan koyon aiki a masana’antar fim ta Kannywood, amma da aka yi haƙuri ba ga shi ya wuce ba. Sannan ga abinda na koya a fannin noma.

By ukarofi