
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Wata babbar kotu a Jihar Kano, ta ce har yanzu sarki Aminu Ado Bayero na riƙe da kambun sarautar dake nuna cewa yana da ikon faɗa-a-ji duk da cewa gwamnatin Jihar ta fitar da sanarwar rusa tsarin masarautun da tsohuwar gwamnati ta yi a baya.
Mai Shari’a Liman Mohammed ya bayyana haka jim-kaɗan bayan wata sanarwa da ta fito daga wata kotun Jiha sakamakon ƙarar da gwamnatin Jihar take kai tana mai cewa Sarki Ado da wasu sarakuna huɗu basu da hurumin amsa sunayen sarakuna tunda gwamnatin Jihar ta soke tsarin masarautunsu da aka yi a zamanin tsohon gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje.
