Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranakun hutun sallah

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnatin Tarayya ta ware ranakun Litinin da Talata a matsayin lokacin hutun bikin Babbar-sallah a faɗin ƙasar.

Babbar sakatariyar ma’aikatar harkokin cikin gida, Dakta Aishetu Gogo Ndayako ta faɗi hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar juma’a.

Dakta Aishetu ta ce, ministan ma’aikatar, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya inda ya ce yana mai taya al’ummar musulmi murnar zagayowar wannan lokaci mai albarka.

Ya kuma yi kira ga al’ummar musulmi da su cigaba da kasancewa masu son zaman lafiya, da kyautatawa juna, da sadaukarwa tare da yin addu’o’in samun zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya.

Olubunmi ya kuma tabbatar da cewa, gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana iya ƙoƙarinta wajen ganin ta samar da tsaro ga rayuka da dokiyoyin al’ummar Najeriya.

By Babaji