
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnan Jihar Zamfara dake Arewa-maso-Yammacin ƙasarnan, Dauda Lawal ya koka kan yadda jami’an ƴan sanda da na soji ke haifar da koma baya wajen ganin an daƙile ayyukan ƴan ta’adda da ke addabar Jihar tsawon lokaci.
Dauda ya ce rashin bin umurnin gwamnatin tarayya ga hukumomin kan matsalar ke da alhakin gefa Jihar cikin mawuyacin halin da take ciki a yau ganin yadda al’umma suka gagara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali tsawon shekaru.
A cikin wata hira da gidan talabijin na ‘channels’ a ranar Talata, ya ce kasancewar bashi da iko kan dukkan ɓangarorin jami’an hakan ya sa yake fuskantar ƙalubale wajen gudanar da lamuran tsaron Jihar.
Ya kuma ƙara da cewa suna fuskantar matsalar siyasantar da ɓangaren harkokin tsaro a faɗin Jihar wanda hakan ke dagula yanayin zaman lafiya al’ummarsu.
Gwamnan ya ƙara da cewa, garkuwa da mutane gami da karɓar kuɗin fansa ya zama ruwa dare inda za’a iya magance matsalar cikin makonni biyu matuƙar an yi amfani da hanyar da ta dace a gwamnatance.
Daga ƙarshe, ya ce akwai wasu ƴan siyasa dake tattaunawa da ƴan bindigan a Jihar ba tare da saninsa ba.
