Ana zargin Babban Sakataren Ma’aikatar Ƙasashen waje da cin zarafin mata

Spread the love

A wani jawabi mai kiɗimarwa, Ministan harkokin ƙasashen waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya rubuta takardar ƙorafi zuwa ga shugabar ma’aikatan Najeriya, Dr Folasade Yemi-Edan, a kan zargin Babban Sakataren ma’aikatar, Ambasada Ibrahim Adanmu Lamuda da cin zarafin wata matar aure ma’aikaciyarsa, Mrs Simisola Fajemirokun.

Ƙorafin yana ƙunshe ne a wata wasiƙa da News Point Nigeria ta samu damar gani, wanda ke ɗauke da kwanan wata 27 ga watan Mayu, 2024, mai taken ” ƘORAFI DANGANE DA CIN ZARAFIN MRS SIMISOLA FAJEMIROKUN AJAYA DA AMBASADA IBRAHIM ADAMU LAMUWA (BABBAN SAKATAREN MA’AITAKAR HARKOKIN KASASHEN WAJE) YA YI”

Wasiƙar, wacce take ɗauke da sa hannun Ministan Ministan harkokin ƙasashen wajen, tana ɗauke da wasu jawabai kamar; “Ya zama min tilas in rubuto domin gabatar da ƙorafi a hukumance a kan Babban Sakataren ma’aikatar harkokin ƙasashen waje, Ambasada Ibrahim Adamu Lamuwa a kan zargin cin zarafi.

“Duba da girman lamarin, na ga dacewar in sanar da ke tare da neman ki ɗauki matakin da ya dace.

“Ga kwafi na takardar ƙoƙafin da aka turo min ta adireshina na yanar gizo. Ina kuma tabbatar maki cewa a shirye nake in bayar da duk wata gudunmawa a gareki don gudanar da aikinki.”

Wata majiya a ma’aikatar wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta sanar da wannan jaridar cewa, wannan ba shi ne karo na farko da Babban Sakataren ya aikata cin zarafin jima’i ga ma’aikaciya matar aure ba.

“Babban Sakataren ya yi cin zarafin jima’i ga wasu matan aure a ma’aikatar. Wannan ba shi ne na farko ba, wani al’amari da ya yi wannan girma y auku a bara kuma manya a ma’aikatar sun yi ƙoƙarin yin rufa-rufa a kai.
majiyar da ƙara da cewa, “Saidai, wasu ma’aikata mata sun yanke shawarar cewa idan har ba a magance wannan matsalar ba, zasu je kotu sannan kuma su kai lamarin da kafafen yaɗa labarai, saboda tura ta kai bango game da wannan cin zarafi da mutumin nan yake masu’,

Da aka tuntuɓeshi dangane da batun, mai bayar da shawara na musamman kan harkokin kafafen yaɗa labarai da sadarwa ga Ministan harkokin ƙasashen wajen, Alkassin Abdulƙadir, kawai ya amsa ne da cewa, ‘da gaske ne’.

Dangane da al’amuran cin zarafin da ya danganci jima’i, sashe na 351 nakundin tsarin mulki na Najeriya, ya ce, “Duk wanda ya ci zarafin wani ba bisa ƙa’ida ba, ya aikata babban laifi, kuma zai fuskanci hukunci, idan ba a samar da babban hukunci ba, zai yi zaman gidan kaso na shekara ɗaya.

By ukarofi