Yadda kotu ta dakatar da EFCC daga kama Kwankwaso

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Wata babbar kotu a Jihar Kano ta fitar da takardar hana kama ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP a babban zaɓen shekarar 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso da wasu mutane bakwai, wacce ke ƙunshe da hana kamawa ko cin mutunci ko kuma tsare su.

Mutanen sun haɗa da Ajuji Ahmed, Dipo Olayanku, Ahmed Balewa, Clement Anele, Folshade Aliu, Buba Galadima da kuma Rabiu Musa Kwankwaso.

Mai Shari’a Yusuf Ubale Muhammad ya fitar da takardar dake ɗauke da bayanin wanda ya fara aiki daga ranar 5 ga watan yunin shekararnan.

Kotun ta ce ta ɗage sauraron ƙarar batun wanda ya shafi hukumar ta EFCC zuwa ranar 24 ga watan yuni.

Sanarwar ta kuma ƙunshi bayanai dake nuni da cewa daga ranar da aka fitar da ita, babu ɗaya daga cikin mutanen da ta ayyana da EFCC zata bincika ko ta kama har sai ta fitar da sakamakon zaman da zata yi nan da ƴan makonni.

Leave a Reply