Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Aisha Adam Hussaini wacce a fagen rubutu aka fi sani da Ameera Adam, ita ce Gwarzuwar Gasar Hikayata ta BBC Hausa ta shekarar 2023. Marubuciyar labaran hikayoyi da almara, wacce Allah Ya yi wa baiwar sarƙafa labari cikin hikima da basira, kai ka ce a zamanin Barbushe take ko cikin Daular Ifiritai. Ƴar baiwa ce ta nunawa a fadar Sarki, domin kuwa babu wata gasar marubuta adabi da ake shiryawa wacce in Aisha ta shiga ba ta samun nasara, don haka ne ma nasarar ta a Gasar Hikayata ba ta zo wa mutane da dama a bazata ba. Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya samu zantawa da ita don jin yadda nasarar da ta samu a Gasar BBC Hausa ta zama mata Gobarar Titi. Da kuma burin da take da shi na kawo sauyi a harkar rubutun adabi. Sai ku gyara zama ku ji yadda tattaunawar tasu ta kasance.
MANHAJA: Ina son ki gabatar mana da kan ki.
AMEERA: Assalamu Alaikum. Da farko dai sunana Aisha Adam Hussaini, wacce aka fi sani da Ameera Adam. Ni marubuciyar littattafan Hausa ce, kuma ɗaliba a Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kano, wato FCE. Sannan ni matar aure ce, ina da yara biyu. Kuma ina zaune ne a garin Kano.
MANHAJA: Ko za ki gaya mana tarihin rayuwarki a taqaice?
AMEERA: Ni dai ‘yar asalin Jihar Kano ce, daga ƙaramar Hukumar Nasarawa.
An haife ni a Unguwar PRP, kuma yanzu haka ina da shekara 28. Na yi karatun boko tun daga firamare har zuwa matakin NCE, yayin da a yanzu nake cigaba da karatuna a matakin Digiri a Kwalejin Ilimi ta Tarayya ta FCE Kano, inda nake nazarin hanyoyin koyar da harshen Turanci. A ɓangaren karatun addini kuwa, na yi daidai gwargwado. Na yi saukar Alqur’ani Mai Girma a shekarar 2013.
MANHAJA: Wanne abu ne ya faru a rayuwarki lokacin tasowarki wanda ya taimaka wajen inganta tarbiyyarki da tunaninki?
AMEERA: Na taso cikin kyakkyawar tarbiyya, ilimi, kulawa, da ƙaunar daga wajen magabatana, waɗanda su ne turakan da suka girka duk wani abu da ya inganta rayuwata. Sakamakon jajircewar da iyaye suka yi don ganin sun sauke nauyin da Allah (S.W.T) Ya ɗora musu.
MANHAJA: Wanne abu ne ya sa ki ka fara sha’awar rubutun adabi?
AMEERA: Na yi karance-karance da dama tun daga irin su Magana Jari Ce, Iliya ɗan Mai ƙarfi da sauransu. A taƙaice dai karance-karancen littattafan Hausa ne, suka ja hankalina nima na fara nawa rubutun a fagen Adabi.
MANHAJA: Ko za ki iya tuna labarin farko da ki ka fara rubutawa?
AMEERA: Da farko dai na fara rubutu ne a shekarar 2012 , a lokacin na rubuta labarin ne a cikin littafi ba a onlayin ba. Sunan littafin shi ne ‘Kwaɗayi Ko Son Zuciya?’ Amma a onlayin, labarin da na fara rubutawa ban kammala shi ba na rasa shi a wayata, dalilin da ya sa ban kammala shi ba kenan. Sai mai biye masa shi ne ‘Yawon Sallar Hajiya Iya,’ shi kuma na rubuta shi ne a shekarar 2019-2020.
MANHAJA: Wane ne ya fara koya miki yadda za ki yi rubutu, ko nuna miki ƙa’idojin rubutu?
AMEERA: A lokacin da na fara rubutu babu wanda ya fara nuna min yadda zan yi rubutu, kuma a lokacin da na fara rubutu babu wanda ya taɓa nuna min yadda zan kiyaye ƙa’idojin rubutu. Sai dai akwai wani zaure a manhajar WhatsApp mai suna Majalisar Marubuta da nake ciki, ina kiyaye yadda manyan marubutan ciki suke rubutunsu bisa tsari. Da zarar na ga sun yi wa wani gyara, zan riqe wannan gyaran da aka yi masa na dinga amfani da shi. A taƙaice dai a wancan lokacin ina koya da kiyaye qa’idojin rubutu, ta hanyar lura da hirar da manyanmu na cikin wannan gidan suke yi. Amma manyan malamaina a yanzu su ne, Malam Jibrin Adamu Rano ne, sai Nana Aicha Hamisu Maraɗi.
MANHAJA:Wacce shekara ki ka fara fitar da rubutunki kuma kawo yanzu littattafai nawa ki ka rubuta?
AMEERA: Na fara fitar da rubutuna a onlayin a shekarar 2015-2016. Na kuma rubuta labarai dogaye 14, da gajerun labarai da dama.
MANHAJA: Gaya mana sunayen littattafanki, kuma ki yi mana bitar fitattu uku a cikinsu.
AMEERA: Littattafan da na rubuta su ne ‘Yawon Sallar Hajiya Iya’, ‘Tsantsar Butulci’,
‘Ɗan Ba Qara’, ‘Aseela’, ‘Marwan’, ‘An Ya Baiwa Ce?’ ‘Dubu Jikar Mai Carbi’,
‘Baƙar Daula’, ‘Zaujatu Jinnul-Ashiq’, ‘Shu’umar Masarauta’, ‘Jariri’, ‘Wanda Bai Ji Bari Ba’, ‘Yar Zaman ɗaki’, da kuma ‘Indo Sarƙa’.
Littafin ‘Shu’umar Masarauta’, labari ne da ya shafi gidan sarauta. Yana ɗauke da tsantsar zaman makirci a tsakanin matan sarki. Zalunci, tsafi, da tsantsar cin amana, sun taka muhimmiyar rawa a cikin labarin. Kuma wata irin masarauta ce mai ɗauke da rikitattun al’amura, musamman da jinsin aljanu ke da ta su fadar a cikin masarautar.
Shi kuma littafin ‘Dubu Jikar Mai Carbi’, yana ɗauke ne da labarin gidan gandu, wanda na rubuta shi cike da zallar barkwanci. Yana nusar da mutane muhimmancin biyayya da haƙuri da iyaye, musamman idan girma ya kama su, da alfanun biyayyar da aka yi a gaba.
Sai kuma akwai littafin da na sa wa suna ‘Jariri’, shi kuma tunatarwa ce da fadakarwa ga mata masu ciki, waɗanda ba su damu da azkar ko addu’o’i ba, musamman idan za su yi wani uzuri da daddare. Labari ne da aka nuna muhimmancin riƙo da addu’a, shi ma akwai barkwanci sosai a ciki.
MANHAJA: Shin kin taɓa buga wani a cikin littattafanki ko duka a onlayin ki ke sakewa?
AMEERA: Ban taɓa buga wani daga cikin littattafaina ba, sai dai ina sa rai a nan gaba, in sha Allah. Gabaɗaya dai labaraina a onlayin nake sakin su.
MANHAJA: Wacce qungiyar marubuta ki ke, kuma wanne taimako Ƙungiyar ke miki a rubuce-rubucenki?
AMEERA: Ina cikin qungiyar First Class Writers Association ne, kuma tana ba ni gudunmawa a ɓangaren rubuce-rubucena. Ƙungiyata tana taimaka min da shawarwari, da sauran ‘yan ƙungiyar, musamman game da abin da ya shafi sanin ƙa’idojin rubutu. Tana kuma taimaka min ta hanyar watsa labaran da nake sakewa idan na rubuta, domin ya watsu a lungu da saƙon cikin onlayin. Ƙungiyata kuma tana qarfafa min gwiwa, domin na cigaba da jajircewa ta fannin rubuce-rubuce.
MANHAJA: Waye a cikin marubuta ya zama miki madubin kwaikwayo a salon rubutunsa ko gogewarsa?
AMEERA: Akwai marubuta da dama da rubutunsu yake birge ni kuma ina ƙaruwa da shi, amma gaskiya ba ni da allon kwaikwayo. Saboda yawanci labaraina sun sha bambam da na marubuta, kamar yadda na faɗa na fi yin rubutu ne a kan abin da ya shafi almara da aljanu.
MANHAJA: Me ya sa ki ke da sha’awar yin rubutun almara irin na aljanu da masarautu?
AMEERA: Na fi sha’awar rubuta labarin almara da na aljanu ne saboda tun asali ire-iren waɗannan labaran ne suka fi birge ni. A gaskiya labarin soyayya bai cika birge ni ba. Sannan dalilin da ya sa kenan nake son labarin masarauta suna qayatar da ni, har wani lokacin ma nakan ga kamar abin ya faru da gaske.
Sannan a lokacin da na fara rubutu labaran aljanu ba su yi yawa kamar yanzu ba, ganin sun yawaita ya sa na sauya akalar labaraina, nake haɗawa da masarautu ina zuba aljanu a ciki.
MANHAJA: Yaya alaƘarki take da masu bibiyar littattafanki, kuma ta yaya ki ke hulɗa da su?
AMEERA: Ina da kyakkyawar alaƙa da masu bibiyar littattafaina, tsakanina da su sai mutumci da mutunta juna. Kuma suna ba ni goyon baya ɗari bisa ɗari ta hanyar sayen littafina. Wani abin farinciki ma kuma suna bayyana min darussan da suke ɗauka a cikin labaraina bayan sun karanta.
MANHAJA: Shin wani makarancin littattafanki ya taɓa baki wata shawara da ta sa har ki ka canza wani tsari da ki ka yi wa labarinki?
AMEERA: Babu shakka ina samun shawarwari da yawa daga masu bibiyar littattafaina, game da wasu labaraina. Sai dai ban taɓa ɗaukar ɗaya da har ya sauya min akalar labarina ba. Saboda ina gama tsara yadda labarina zai kasance, tun daga farko har ƙarshe.
Idan na duba shawarwarin da suke bayarwa yawancin abin da suke so ya faru a cikin labarin ne saɓanin yadda na tsara shi. Ko a kwanaki hakan ya faru a littafin da na gama ‘Shu’umar Masarauta,’ da yawa ba su ji daɗin kisan da na yi wa wata jigo a cikin labarin ba, duk da shawarwarin da suka bayar.
MANHAJA: Yaya ki ke samun jigo ko basirar yin rubutunki?
AMEERA: Akasari ina samun jigon rubutuna ta hanyar nazari da tunani ne, sai kuma idan ina kallon finafinai, musamman na ban tsoro da al’ajabi.
MANHAJA: Wanne littafi ne rubutunsa ya fi baki wahala, kuma wanne ne ya fi miki sauƙin kammalawa, mene ne dalili?
AMEERA: Labarin ‘Baqar Daula’ ne ya fi ba ni wahalar rubutu, saboda labarin a kan Maharba da Mafarauta ne. Kuma labarin yana da sarƙaƙiya sosai, ga shi salon tafiyar kura ne. Shi kuma labarin ‘Zaujatu Jinnul-Ashiq’ shi ne labarin da ya fi min sauƙin rubutu, saboda labari ne da ya danganci mu’amalar mutane da Aljanu. Kishi ne mai zafi tsakanin matar Aljani da Bil’adam. Ina son labaran abin da ya shafi Aljanu da almara. Shi ya sa labarin ya yi min sauƙin rubutu.
MANHAJA: Kina daga cikin gwarazan Gasar Hikayata ta BBC Hausa na 2023, gaya mana sirrin samun nasarar ki, kuma sau nawa ki ka shiga gasar?
AMEERA: Sirrin gasar Hikayata ta BBC Hausa addu’a ce da jajircewa. Duk wacce za ta shiga gasar Hikayata ta yi rubutu mai kyau, ta kuma ɗauki jigo mai kyau ta yi rubutu a kansa. Bayan ta rubuta sai ta bai wa masana su duba mata, sannan ta bi ta da addu’a bakin gwargwadon ikonta.
Na shiga gasar BBC Hausa har karo uku. Sau biyun da na yi labarina bai taɓa zuwa matakin farko ba, sai a shekarar da ta gabata ta 2023 ne Allah Ya ƙaddara.
MANHAJA: Wanne canji wannan nasara ta kawo a rayuwarki?
AMEERA:Nasarar gasar BBC Hausa ta kawo sauyi da dama a cikin rayuwata, ciki kuwa har da ɗaukakar da ni da wani nawa ma bai taɓa tsammani ba. Silar gasar na samu alheri mai ɗimbin yawa, kuma na haɗu da mutanen da ko a duniyar mafarki ban taɓa tsammani ba.
MANHAJA: Ban da Gasar Hikayata, kin taɓa samun nasara a wasu gasanni da ake shiryawa?
AMEERA: Alhamdulillahi. Na yi nasara a gasanni da dama a ciki akwai gasar zauren Marubuta na WhatsApp a shekarar 2021. Na samu nasarar zama ta ɗaya da labarina mai suna ‘Adabin Maƙaryata.’ Akwai kuma gasar ƙungiyar mu ta Perfect Writers Association, inda na zo ta uku a 2022, da labarina mai suna ‘ƙaddarar Rufaida.’ A 2023 ma na samu nasarar zama ta biyu a gasar Dikko Raɗɗa ta ‘Mun Gani A qasa, wacce na shiga da labarina ‘Tudun Tsira’. Duk dai a shekarar 2023 na zama ta biyu a Gasar Auren marubuciya Bilkisu da labarina mai taken ‘Abincin Wani’.
MANHAJA: Yaya ki ke ganin girman matsalar da masu satar fasaha suke haifar wa marubuta? Ko ke ma an taɓa sace miki labari?
AMEERA: Babu shakka an tavɓa sace min wani labarina wanda na sa wa suna ‘Baqar Daula’. Sai kawai na ga wani ya ɗora shi a wani zauren yanar gizo. Amma da na yi masa magana ya sauke. A gaskiya hakan babbar illa ce ga marubuta, kuma yana dakushe wani ɓangare na samunsu, saɓanin da su za su wallafa abin su, tun da haƙƙin mallakarsu ne.
MANHAJA: Menene burinki nan gaba a matsayinki na marubuciya?
AMEERA: Babban burina na zama marubuciyar da duk duniya za a santa, kuma harshen Hausa ya ci gaba da alfahari da ni.
MANHAJA: Wanne abu ne ya fi damunki a harkar rubutu da ki ke so in kin samu dama ki kawo gyara?
AMEERA: Rubutun batsa shi ne abin da ya fi ci mini tuwo a Ƙwarya, da ina da wata dama shi ne abu na farko da zan fara dakatarwa. Domin babu wani alkairi da yake kawowa a cikin al’umma, illa ɓata mana suna da suke yi domin ana yi mana kuɗin goro da su. Kuma babban hatsari ne ga rayuwar ƙannenmu ƙanana masu tasowa. Sai kuma kawo hanyar da marubuci zai inganta rubutunsa, ta yadda zai dinga samun kuɗin shiga ba tare da ya samu matsala da masu sayen littafi suna fitar da shi ba.
MANHAJA: Kina ganin akwai wata rawa da gwamnati za ta iya takawa don kawo cigaba a harkar rubutun adabi?
AMEERA: Da a ce gwamnati za ta ja marubuta jiki ta ba su muƙamai kamar yadda take rabawa sauran masana’antu, kuma ta saurare su ta ji matsalolinsu da buƙatunsu. Ina ganin za ta taka muhimmiyar rawar da za ta kawo cigaba a fagen rubutun adabi da rayuwar marubuta.
MANHAJA: Kin taɓa yin rubutun fim ko kina da sha’awar rubutawa nan gaba?
AMEERA: Na taɓa rubuta labarin fim mai suna ‘Qalubale’, kuma ina da fatan nan gaba idan an sake samun gogewa zan cigaba da rubutawa.
MANHAJA: Wanne abu ne ya fi faranta miki rai a mu’amalarki da marubuta?
AMEERA: Haɗin kan marubuta, zumuncinsu da yadda suke mu’amalantar juna yana matuƙar saka ni nishaɗi.
MANHAJA: Wanne abu ne ya fi sa miki nishaɗi a rayuwarki?
AMEERA: Abin da ya fi saka ni nishaxɗi a rayuwa na wayi gari ni da iyalina muna cikin ƙoshin lafiya, kuma ya kasance da ‘yan canji a tare da ni.
MANHAJA: Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?
AMEERA: Karin magana uku ne suke tasiri a rayuwata.’Dogaro ga Allah jari. Sai ‘Mahaƙurci mawadaci,’ da ‘Mai nema yana tare da samu.’
Masha Allah. Na gode.
Ni ce da godiya.