Sabbin hare-haren Isra’ila a Rafah sun sake fusata duniya – Shawesh

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jakadan Falasɗinu a Nijeriya, Abdullah Abu Shawesh ya bayyana cewa a rana ta 237 da aka fara kisan ƙare dangi a kan al’ummar Falasɗinu, a bayyana yake ƙarara cewa ana amfani da dokokin ƙasa da ƙasa ne kawai a ƙasashen kudanci.
Abu Shawesh ya bayyana hakan ne a wata sanarwar manema labarai da ya fitar, ranar Alhamis.
Ya ce, “ya zuwa ranar Talata 29 ga watan Mayu, an samu Falastinawa shahidai 36,096 da kuma 81,136 da suka jikkata, inda kusan dubu 10 suka ɓace a qarqashin ɓaraguzan ginin da ƙungiyoyin ceto ba su yi nasarar kai wa ba wuraren su.
“Yakin Gaza kaɗai ya laqume rayukan ma’aikatan jinƙai sama da 224, ciki har da na UNRWA sama da 190, da sauran ma’aikatan hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya. Ma’aikatan ƙasa sun kasance mafi rinjaye – sama da kashi 90 cikin ɗari – na waɗanda abin ya shafa a Gaza da sauran rikice-rikice.
Ya ƙara da cewa, “ƙasashen duniya sun yi Allah wadai, kan harin da Isra’ila ta kai wani sansanin Falasɗinawa da suka rasa matsugunansu, da ke kusa da garin Rafah a kudancin Gaza, har ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
“Tuni dai ƙungiyar Tarayyar Turai EU, ta bakin babban jami’in kula da harkokin wajenta, ta yi Allah wadai da harin.
“Babban Jami’in ya bayyana hakan ne a shafinsa na X, inda ya ce, qungiyar ta EU, ta bayyana faragabarta matuka bayan samun labarin harin, domin a cewarta rashin Imani da rashin tausayi ne tsantsa, irin hare-haren da Isra’ila ke yi a Rafa.
“Ta ce, yanzu haka babu wani wuri mai aminci a Gaza, saboda haka dole ne Isra’ilan ta dakatar da hare-haren nan take.
Da yake ambaton ƙwararrun Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce, “Dole ne a daina kai makamai zuwa cikin Isra’ila nan take. A bayyane yake cewa ana amfani da waɗannan makamai ne wajen kisan gilla da kuma raunata fararen hula a Falasɗinu.”
“Kashi biyar cikin ɗari na al’ummar Gaza an kashe ko kuma sun jikkata, fiye da kashi 70 cikin 100 na gidajen da aka lalata, sannan fiye da kashi 75 cikin ɗari na sun rabu da muhallansu. Dole ne a kawo ƙarshen kisan kai ga mutanen Gaza.”
“Ya zuwa ranar 26 ga Mayu, adadin Falastinawa da aka kama tun ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 8,875 a yankin Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye da kuma Kudus da suka haɗa da mata 295, yara 630 da ’yan jarida 76. 5900 daga cikinsu suna ƙarqashin umarnin qasa. Fursunoni 18 ne suka yi shahada a gidajen yari da sansanonin soji na Isra’ila, inda har yanzu ba a karɓo gawarwakinsu ba.
“Fursunonin Falastinawa suna fuskantar muguwar azaba da azabtarwa a gidajen yarin Isra’ila,” inji Abu Shawesh.

Leave a Reply