15
Jul
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dattawa na shirin samar da wani tsari domin kula da lamuran halarta da hazaƙar sanatoci a yayin zaman majalisa, a matsayin wani ɓangare na ƙarfafa ƙoƙarinsu a harkokinta. Sanata Abdul Ningi (Jihar Bauchi) ne ya gabatar da buƙatar a ranar Laraba, inda nemi shugabancin majalisar da ta riƙa tattara rahoton halarta da gudunmawa yayin muhawara akan muhimman batutuwan majalisa. A cewarsa, yana da kyau a riƙa tantance wa da wa ne suke ƙoƙarin bayar da gudunmawa a majalisar domin ƙara wa mambobin ƙwarin-gwiwar tofa albarkacin baki da yin abin da ya dace akan…
