Babaji

4771 Posts

Da Ɗumi-Ɗumi: ‘Yan sanda sun kama Darakta Janar na hukumar bogi, Adeyemi bayan kotu ta bada izinin kama shi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jami'an tsaro sun kama Adeniyi Adeyemi, wato wanda ya kira kansa da Darakta Janar na hukumar bogi ta PFIPC. Hakan na zuwa ne bayan da Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bayar da izinin kama shi. Rahotanni sun bayyana cewa, an yi zargin cewa an cafke Adeyemi ne a maɓoyarsa ta Jihar Osun, inda ake sa ran kai shi Hedikwatar Rundunar 'Yan sanda a Abuja, ranar Talata. Babu cikakken bayani game da yadda aka kama shi a lokacin haɗa wannan rahoto. Hakan na zuwa ne sa'o'i bayan Mai Shari'a Mohammed Umar ya umarci a…
Read More

Badaƙalar hukumar bogi: Adeyemi bai halarci zaman kotu ba yayin da aka shirya gurfanar da shi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An dakatar da sauraron ƙarar da aka shigar akan Darakta Janar na hukumar bogi ta PFIPC, Adeniyi Adeyemi sakamakon rashin bayyanarsa a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Talata. Ana sa ran ganin Adeyemi ya bayyana a gaban Alƙali Mohammed Umar ne kan tuhume-tuhume guda takwas da suka shafi zarge-zargen bogi, damfara da sojan gona da aka shirya gabatarwa akansa. Ana ganin Sufeto Janar na Rundunar 'Yan sanda da ya shigar da ƙarar akan Adeyemi, ya nemi kotun ta bayar da izini domin kamo shi a duk inda yake. A ranar…
Read More

Za a kammala kwaso ‘yan Nijeriya a Afirka ta Kudu gobe yayin da 315 suka rage

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jimillar 'yan Nijeriya guda 315 da suke cikin halin matsi a ƙasar Afirkata Kudu ne rukunin ƙarshe daga cikin waɗanda Gwamnatin Nijeriya take ƙoƙarin tabbatar da dawo da su gida bayan hare-haren ƙyamar baƙi da suka riƙa fuskanta a sassan ƙasar. Ana sa ran jirgin ƙarshe da zai yi jigilar 'yan Nijeriyar ya bar Afirka ta Kudu da misalin ƙarfe 1:30 na dare, inda ake sa ran ya iso Filin Murtala Muhammed da ke Legas da mislain ƙarfe 6:30 na safe. Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Nijeriya, Kimiebi Imomotimi Ebienfa ne ya sanar da haka…
Read More

Birtaniya ta sanya sabbin sharuɗɗan shiga ƙasarta ga ‘yan Nijeriya da wasu ƙasashen Afirka 32

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙasar Birtaniya ta umarci Nijeriya da wasu ƙasashen Afirka guda 32 da su mallaki takardar tantancewa ta shiga gabanin zuwa ko wucewa ta ƙasar. Birtaniya ta sanar da haka ne ta ofishin hukumar shige da ficenta a ranar Litinin. Sabon jaddawalin sharuɗɗan ya ƙunshi matafiya su tabbatar da cika ƙa'idojin biyan ƙudin jirgin zuwa ƙasar, inda ta yi gargaɗin cewa waɗanda ba su da takardun da ake buƙata ka iya fuskantar jinkiri ko soke tafiyarsu. Haka kuma, 'yan ƙasashe sama da 100 da yankunan ake buƙatar su mallaki biza gabanin shiga Ingila da nufin…
Read More

Badaƙalar hukumar bogi: Adeyemi ya buƙaci Tinubu ya sanya wakilan manyan ƙasashen waje cikin kwamitin bincike

Adeniyi Adeyemi, wanda ke iƙirarin cewa shi ne Darakta Janar na abin da ya kira Hukumar Bunƙasa Zuba Jarin Ƙasashen Waje ta Fadar Shugaban Ƙasa (PFIPC), ya rubuta buɗaɗɗiyar wasiƙa ga Shugaba Bola Tinubu inda ya buƙaci a kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin binciken takaddamar da ta dabaibaye hukumar. A cewarsa, ya kamata kwamitin ya haɗa da wakilan Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), Amurka, Birtaniya, Tarayyar Turai, ECOWAS, AU, ƙungiyoyin fararen hula da masu sa ido na ƙasa da ƙasa domin tabbatar da gaskiya da amincewar jama'a. Rahotanni sun bayyana cewa, Adeyemi ya ce ba zai amince ICPC ita…
Read More

Amurka da Iran sun yi musayar wuta a mashigar Hormuz

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kasar Iran ta ce ta ƙaddamar da hare-hare akan wasu manyan jiragen dakon mai a yankin mashigar Hormuz da ke gaɓar ruwan iyakarta Dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran sun ce suna kai hare-hare kan ne akan jiragen da kuma wuraren da ke da alaƙa da Amurka a ƙasar Bahrain, yayin da rikici a tsakanin ƙasashen biyu ya sake caɓewa. Dakarun sun ce, sun lalata wasu jiragen ruwan dakon mai bayan sun yi watsi da gargaɗin da aka yi musu tare da kashe na’urorin da ke nuna inda suke zirga-zirga. A nata ɓangaren,…
Read More

Sojoji sun samu muhimman bayanan ISWAP bayan halaka mai ɗaukar hotonsu

Dakarun Atisayen Haɗin Kai sun sanar da halaka wani mai ɗaukar bidiyo na ƙungiyar ISWAP tare da gano bayanai masu nuna cewa wasu baƙi 'yan ƙasashen waje uku na taimaka wa ƙungiyar a Jihar Borno. Kakakin rundunar na Arewa maso Gabas, Kyaftin Muhammed Goni ya ce al'amarin ya faru ne bayan dakarun sun daƙile wani yunƙurin da mayaƙan ISWAP suka yi na kutsawa Cross Kauwa da ke ƙaramar hukumar Kukawa a daren Asabar wayewar Lahadi domin sace kayan maganin cutar kwalara a yankin. A cewarsa, dakarun sun gano motsin 'yan ta'addan ne akan lokaci tare da buɗe musu wuta, lamarin…
Read More

Kotu ba ta soke zaɓukan fidda gwanin ADC ba, inji Atiku yayin da ya garzaya Kotun Ƙoli

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi watsi da iƙirarin cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke zaɓukan fidda gwani na jam'iyyar da aka gudanar domin babban zaɓen 2027, yana mai bayyana rahoton a matsayin ƙarya da ke ƙoƙarin ruɗar da 'yan Nijeriya da raunana ɓangaren adawa. Atiku, a wata takarda da Mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu ya fitar a ranar Litinin, ya yi kira ga mambobin ADC da magoya baya a sassan Nijeriya da su kwantar da hankali tare da cigaba…
Read More

Hedimastan Oyo ya shaƙi iskar ‘yanci sa’o’i bayan sace shi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hedimastan makarantar Nomadic Basic School da ke Igbojaye a Ƙaramar Hukumar Itesiwaju ta Jihar Oyo, Mista Mathew Kolawale Owoade ya shaƙi iskar 'yan bayan garkuwa da shi da aka yi na tsawon kusan sa'o'i 48. An sako hedimastan mai shekaru 60 ne da misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar Litinin, 13 ga Yuli, 2026. Da fari, masu garkuwar sun buƙaci a biya Naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa, inda iyalan suka yi magiya akan su karɓi miliyan N3, wanda da farko sun amince. Bayan iyalan sun tara miliyan N3, an yi zargin cewa…
Read More

Sojoji sun miƙa ɗalibai da malaman Oriire da aka ceto ga gwamnatin Oyo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar Sojin Nijeriya ta miƙa ɗalibai da malaman nan da aka sace na makarantu a yankin Oriire da ke Jihar Oyo ga gwamnatin jihar a hukumance bayan kammala aikin duba lafiyarsu da nazari a kai a sa'ilin da aka ceto su. A ranar, Juma'a, 10 ga Yuli, 2026 ne suka shaƙi iskar 'yanci bayan shafe kwanaki 56 a hannun 'yan bindiga. An damƙa su ne bayan sama da kwanaki biyu ana musu magani a Asibitin Shiyya ta 2 ta hedikwatar Rundunar Sojin da ke Barikin Odogbo a Ibadan. Wannan na nufin kawo ƙarshen aikin…
Read More