Babaji

4774 Posts

Kotu ba ta soke zaɓukan fidda gwanin ADC ba, inji Atiku yayin da ya garzaya Kotun Ƙoli

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi watsi da iƙirarin cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke zaɓukan fidda gwani na jam'iyyar da aka gudanar domin babban zaɓen 2027, yana mai bayyana rahoton a matsayin ƙarya da ke ƙoƙarin ruɗar da 'yan Nijeriya da raunana ɓangaren adawa. Atiku, a wata takarda da Mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu ya fitar a ranar Litinin, ya yi kira ga mambobin ADC da magoya baya a sassan Nijeriya da su kwantar da hankali tare da cigaba…
Read More

Hedimastan Oyo ya shaƙi iskar ‘yanci sa’o’i bayan sace shi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hedimastan makarantar Nomadic Basic School da ke Igbojaye a Ƙaramar Hukumar Itesiwaju ta Jihar Oyo, Mista Mathew Kolawale Owoade ya shaƙi iskar 'yan bayan garkuwa da shi da aka yi na tsawon kusan sa'o'i 48. An sako hedimastan mai shekaru 60 ne da misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar Litinin, 13 ga Yuli, 2026. Da fari, masu garkuwar sun buƙaci a biya Naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa, inda iyalan suka yi magiya akan su karɓi miliyan N3, wanda da farko sun amince. Bayan iyalan sun tara miliyan N3, an yi zargin cewa…
Read More

Sojoji sun miƙa ɗalibai da malaman Oriire da aka ceto ga gwamnatin Oyo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar Sojin Nijeriya ta miƙa ɗalibai da malaman nan da aka sace na makarantu a yankin Oriire da ke Jihar Oyo ga gwamnatin jihar a hukumance bayan kammala aikin duba lafiyarsu da nazari a kai a sa'ilin da aka ceto su. A ranar, Juma'a, 10 ga Yuli, 2026 ne suka shaƙi iskar 'yanci bayan shafe kwanaki 56 a hannun 'yan bindiga. An damƙa su ne bayan sama da kwanaki biyu ana musu magani a Asibitin Shiyya ta 2 ta hedikwatar Rundunar Sojin da ke Barikin Odogbo a Ibadan. Wannan na nufin kawo ƙarshen aikin…
Read More

Kotu ta bada belin Nnaji akan miliyan N20 da ƙwace fasfonsa bayan musanta zarge-zargen da ake masa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta bayar da belin tsohon Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji akan Naira miliyan 20 bayan ya musanta tuhume-tuhume guda shida da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta shigar akansa kan zargin amfani da takardar shaidar karatu ta bogi da kuma sauya akalar kuɗaɗen al'umma. A yayin Shari'ar, Alƙali Joyce Abdulmalik ta umarci Nnaji da ya gabatar da mai tsaya masa guda ɗaya wanda wajibi me ya zama ma'aikacin Gwamnatin Tarayya mai matsayi daga mataki na 15 zuwa sama, tare da wasu sharuɗɗan kotu. Baya…
Read More

Tinubu ya umarci NIMC ta yi wa dukkan ‘yan Nijeriya rajista nan da ƙarshen 2026

A ranar Litinin Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar Kula da lamuran Shaidar Ƙasa ta (NIMC) da ta tabbatar an yi wa baki ɗaya ’yan Nijeriya rajistar shaidar zama ɗan ƙasa kafin ƙarshen shekarar 2026. Wannan umarni ɗaya ne daga cikin ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na gina cikakken tsarin tantance ’yan ƙasa domin inganta gudanar da mulki, tsare-tsaren gwamnati, da kuma sauƙaƙa isar da ayyuka da tallafin gwamnati ga al’umma. Ana sa ran wannan shiri zai taimaka wajen samar da ingantaccen bayanan ’yan ƙasa, ƙarfafa tsaro, bunƙasa tattalin arziki, da kuma tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya yana da cikakkiyar shaidar…
Read More

NDLEA ta kama ‘yar Afirka ta Kudu a filin jiragen saman Abuja ɗauke da miyagun ƙwayoyi

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), ta kama wata 'yar ƙasar Afirka ta Kudu mai shekara 38, Will Jessica Ann, a Filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja bisa zargin ta da shigo da kilogram 5.75 na miyagun ƙwayoyi zuwa Nijeriya. A cewar NDLEA, an kama matar ne a ranar 6 ga Yulin 2026 bayan ta iso daga Doha na ƙasar Qatar tare da ɗanta mai shekara uku. Hukumar ta ce ta ɓoye ƙwayoyin a cikin akwatuna biyu, kuma da farko ta musanta mallakarsu kafin daga bisani ta amsa cewa nata ne. NDLEA ta kuma ce…
Read More

Rikicin ADC ya caɓe bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta haramta wa INEC tabbatar da jagorancin tsagin su David Mark

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, ta jaddada hukuncin haramta wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) amincewa ko karɓar kowane babban taro da shugabancin jam'iyyar ADC na tsagin su David Mark ya jagoranta. A wani zama da kotun ta gudanar a ranar Litinin, ta sake jaddada hukuncin Babbar Kotun Tarayya da aka gudanar a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Joyce Abdulmalik a Abuja. Hukuncin, wanda aka gabatar a ranar 29 ga watan Afrilun 2026, ya haramta wa INEC tabbatarwa ko karɓar kowane ɗaya daga cikin tarukan ƙasa da shugabancin David Mark ya jagoranta daga ɓangaren jam'iyyar…
Read More

Tinubu, Sarkin Musulmi, Sarkin Zazzau, Etsu Nupe, Ministan Labarai da wasu sun halarci taron tseren dawakai a Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Asabar ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci tawagar sarakunan gargajiya, manyan jami'an gwamnati da masu sha'awar wasan tseren doki a babban taron tseren dawakai na yammacin Afirka da aka gudanar a filin Murtala Muhammed da ke cikin garin Kaduna. Gwamna Uba Sani na jihar ne ya wakilci Shugaban Ƙasar a taron karo na biyu, wato na Renewed Hope 2nd West Africa Horse Racing Derby. Taron ya sami halartar Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, wanda ya wakilci Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III; Oluwo na Iwo, Oba Abdulrasheed…
Read More

‘Yan bindiga sun sace shugaban makaranta a Oyo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi awon-gaba da wani hedimasta mai suna Owoade Mathew Kolawale a garij Igbojaye da ke Ƙaramar Hukumar Itesiwaju ta jihar Oyo. An gano cewa, 'yan bindiga sun sace hedimastan mai kimanin shekaru 60 na makarantar Nomadic Basic School ne a yammacin ranar Asabar da tsakanin ƙarfe 5 zuwa 6. A cewar ɗansa, Mista Owoade Abiola, an yi garkuwa da mahaifin nasa ne a lokacin da yake kan hanyar koma wa gida daga gona. Majiyoyi sun ce jim-kaɗan bayan faruwar al'amarin, masu garkuwar sun kira iyalan dattijon…
Read More

ICPC ta gurfanar da tsohon minista, Uche Nnaji

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Litinin Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta gurfanar da tsohon Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zarge-zargen da suka shafi amfani da takardun karatu na bogi da karkatar da akalar kuɗaɗen al'umma. A cewar hukumar, tuhume-tuhume guda huɗu na da alaƙa ne da zargin amfani da takardun karatu na bogi da bayar da bayanai na ƙarya akan hidimarsa ta ƙasa, yayin da sauran biyun kuma suka shafi karkatar da kuɗaɗe a lokacin da yake minista. Saidai, tsohon ministan ya…
Read More