13
Jul
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Litinin Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta gurfanar da tsohon Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zarge-zargen da suka shafi amfani da takardun karatu na bogi da karkatar da akalar kuɗaɗen al'umma. A cewar hukumar, tuhume-tuhume guda huɗu na da alaƙa ne da zargin amfani da takardun karatu na bogi da bayar da bayanai na ƙarya akan hidimarsa ta ƙasa, yayin da sauran biyun kuma suka shafi karkatar da kuɗaɗe a lokacin da yake minista. Saidai, tsohon ministan ya…
