Babaji

4776 Posts

Gwamnatin Tarayya ta amince da N50,000 a matsayin sabon kuɗin jarrabawar WAEC da NECO daga 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta amince da N50,000 a matsayin sabon ƙayyadadden farashin jarrabawar WAEC da ta NECO ga ɗaliban da ke shirin kammala karatun makarantun sakandare, wanda zai fara aiki daga shekarar 2027. Rahotanni sun bayyana cewa, hakan ya biyo bayan buƙatar da Hukumar Shirya Jarrabawar Ɗaliban Ƙasashen Yammacin Afirka (WAEC) ta gabatar ta neman a ƙara kuɗin jarrabawar kammala sakandare (SSCE) ga ɗalibai. Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da ke ɗauke da kwanan wata; 18 ga Yuni, 2026 da Daraktan Ilimin Babbar Sakandare na Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya, Adeniji Ibrahim ya sanya…
Read More

2027: Abin da ya sa Tinubu ya riƙe Shettima a matsayin abokin tafiyarsa – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fadar Shugaban Ƙasa, Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas da jagororin jam'iyyar APC a Arewa maso Gabas, sun kare matakin Shugaba Bola Tinubu na sake ɗaukar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a matsayin abokin tafiyarsa a zaɓen 2027 da ke cigaba da ƙaratowa. Sun bayyana hakan a matsayin sakamakon biyayya, ƙwarewar aiki, da ƙoƙarin hidimta wa ƙasa daga ɓangaren Shettima bisa jajircewa da dattako. Yayin da fadar shugaban ƙasar ta ce yarda da tabbacin cigaba da mulkin Tinubu akan mataimakin nasa ne suka sa shi ɗaukar matakin, Tajudeen Abbas ya ce gamsuwa da Shettima daga…
Read More

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi watsi da buƙatar belin tsohon AGF na riƙo, Nwabuoku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, ta yi watsi da buƙatar bayar da beli da tsohon muƙaddashin Akanta Janar na Ƙasa (AGF), Anamekwe Nwabuoku ya gabatar domin a sako shi daga gidan yari. A ranar 23 ga Maris ne Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Nwabuoku hukuncin ɗaurin shekaru 72 bayan samun sa da hannu a laifukan dq suka shafi halasta kuɗaɗen haram da almundahanar wasu maƙudan kuɗaɗe da adadinsu ya kai miliyan N868.4. Mai shari'a James Omotosho ya bayyana cewa Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, ta gabatar…
Read More

Keyamo ya umarci FAAN ta ci tarar Obi N20,000 bisa ajiye mota ba bisa doka ba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Sufurin Jiragen Sama da Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya ce ya umarci Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN) da ta ci tarar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi Naira 25,000 saboda ajiye motarsa ba a inda ya dace ba a filin jiragen sama na Abuja. Keyamo ya buƙaci da ɗan takarar shugaban ƙasar da ya nemi gafarar ma’aikatan filin jirgin akan zargin da ya yi musu na cewa sun takura masa "ba bisa ƙa'ida ba", lamarin da ya haifar da cece-kuce a fagen siyasa. Obi ya yi…
Read More

Nan ba da jimawa ba safarar ɗan-adam za ta zama tarihi – Gidauniyar FIAP yayin ganawar wakilan Sifaniya da Nijeriya

Gidauniyar Ƙasa da Ƙasa ta Bunƙasa Harkokin Gudanar da Ayyukan Gwamnati (FIAP) ta bayyana cewa, ana sa ran masu safarar mutane da masu fasa-ƙwaurin baƙin haure za su fuskanci tsauraran matakan jami'an tsaron haɗin gwiwa. FIAP ta faɗi haka ne bayan kammala wani taron horaswa na kwanaki huɗu da aka shirya domin ƙarfafa binciken laifukan ƙetare iyakokin ƙasashe da suka shafi Safarar Mutane (TIP) da Fasa-ƙwaurin Bakin Haure (SOM). Javier Leon, Mataimakin Shugaban Tawaga a FIAP kuma Babban Sufeto na Rundunar 'Yan Sandan Ƙasar Sifaniya, ya ce mahalarta taron sun kammala horaswar mai zurfi ne da ƙarin ƙwarewa kan sabbin…
Read More

2027: Tinubu zai samu gagarumar nasara a arewa kan sake ɗaukar Shettima a matsayin abokin tafiya, inji Iliyasu Kwankwaso

Sake ɗaukar Sanata Kashim Shettima da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a matsayin maitaimakinsa a zaɓen shekarar 2027 ya tabbatar wa Jam'iyyar APC sake samun gagarumar nasara a Arewacin Nijeriya domin kusan kowa zai sake zaɓen su domin cigaba da ayyukan raya ƙasa kasa, kamar yadda Babban Daraktan Kudi da Gudanarwa na Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama'are ya bayyana. Ya ce, wannan abin murna ne ga yankin Arewa baki ɗaya musamman ganin yadda shugaban ya fifita tafiyar Musulmi da Musulmi. Shugaba Tinubu ya miƙa form ɗinsa na sake tsayawa takarar Shugaban Kasa ga babban Kwamitin Jam'iyyar APC a…
Read More

APC ta yi hasashen gagarumar nasara bayan riƙe Shettima a matsayin abokin tafiyar Tinubu a zaɓen 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Juma'a Jam'iyya mai mulki (APC) ta sanar a hukumance cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne abokin tafiyar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, tana mai bayyana ƙwarin-gwiwar samun gagarumar nasara. APC ta tabbatar da haka ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce ta karɓi fom ɗinsu na tsaya wa takarar shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen da ke cigaba da kusantowa. Shugaban jam’iyyar na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ne ya karɓi takardun da aka cike wa shugabannin a wani…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar da sako ɗalibai da malaman Oyo da aka sace

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar da ceto baki ɗaya malamai da ɗalibai makarantar Orire ta Ogbomoso da aka yi garkuwa da su a Jihar Oyo. Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga me ya bayyana haka ta kafar X a ranar Juma'a. Ya ce, hukumomin tsaro sun yi nasara ceto dukkanin waɗanda al'amarin ya shafa, lamarin da yak awo ƙarshen rashin tabbas game da halin awon-gaba da su. Saidai, Fadar ba ta bayar da karin bayani akan yadda aka ƙaddamar da atisayen ceto mutanen ba. Haka kuma, hukumomin tsaro ba su fitar da wani saƙo na…
Read More

Ruftawar gini ya rutsa da mutane huɗu a Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Aƙalla mutane huɗu ne suka maƙale bayan wani ginin bene mai hawa biyu da ake kan ginawa ya rufta a yankin titin Sultan da ke birnin Kano da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar ranar Juma'a. Rahotanni sun bayyana cewa, an yi nasarar ceto mutum uku daga ƙarƙashin baraguzan ginin, yayin da ake cigaba da ƙoƙarin ceto mutum na huɗu da al'amarin ya rutsa da su. Shaidun sun bayyana cewa ma'aikatan ginin sun lura da alamun cewa ginin na shirin ruftawa yayin da suke aiki a bene na sama, lamarin da ya sa suka yi…
Read More

Borno: Harin Boko Haram tsakar dare ya yi ajalin amarya da wasu biyu a sansanonin sojoji

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun ƙaddamar da hare-hare a sansanonin sojoji guda biyu da ke Maiduguri a Jihar Borno, lamarin da ya yi ajalin mutane uku. Rahotanni sun bayyana cewa, maharan sun kai farmakin ne da misalin ƙarfe 2:14 na daren wayewar Juma'a a sansanin Kofa, kana daga nan suka zarce zuwa wani wajen sojoji a yankin Muna da ƙarfe 2:30. Shaidu da mazauna yankunan da al'amarin ya shafa sun ce maharan sun kutsa ne akan babura, inda suka riƙa harbe-harbe na kan-mai-uwa da wabi, lamarin da ya rikita jama'a…
Read More