Babaji

4777 Posts

Borno: Harin Boko Haram tsakar dare ya yi ajalin amarya da wasu biyu a sansanonin sojoji

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun ƙaddamar da hare-hare a sansanonin sojoji guda biyu da ke Maiduguri a Jihar Borno, lamarin da ya yi ajalin mutane uku. Rahotanni sun bayyana cewa, maharan sun kai farmakin ne da misalin ƙarfe 2:14 na daren wayewar Juma'a a sansanin Kofa, kana daga nan suka zarce zuwa wani wajen sojoji a yankin Muna da ƙarfe 2:30. Shaidu da mazauna yankunan da al'amarin ya shafa sun ce maharan sun kutsa ne akan babura, inda suka riƙa harbe-harbe na kan-mai-uwa da wabi, lamarin da ya rikita jama'a…
Read More

Kofin Duniya: An yi waje da baki ɗaya ƙasashen Afirka tara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Bajintar da Moroko ta riƙa nunawa a gasar Kofin Duniya na 2026 ya zo ƙarshe bayan shan kaye 2 da 0 a hannun Faransa a wasan kwata fainal, lamarin da ya kawo ƙarshen cigaba da fafatawa da ƙasashen Nahiyar Afirka a gasar. Tawagar Atalsa Lions ta Moroko ce kaɗai ta samu damar kaiwa matakin daga cikin ƙasashen Afirka bayan ɗauki ba daɗi da ita daga tawagogin ƙasashe daban-daban na wasu nahiyoyi. Ƙasashen Afirka guda tara ne suka samu kaiwa zagayen 'yan 32 bayan kammala na rukunin-rukuni, inda a lokacin ne aka cire "DR Congo,…
Read More

Dakatarwar da JAMB ta yi wa ɗaliba Mmesoma kan sakamakon UTME na bogi za ta ƙare a ƙarshen Yuli

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ƙarshen watan Yulin 2026 ne ake sa ran dakatarwar da Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta yi wa ɗaliba Mmesoma Ejikeme za ta ƙare a hukumance, bayan samun ta da laifin sauya ainihin sakamakon jarrabawarta ta UTME na 2023 da na bogi. A shekarar 2023 ne al'umma suka shiga cece-kuce akan Mmesoma bayan ta yi iƙirarin cin 362 a UTME, sakamakon da da zai sanya ta cikin waɗanda suka fi samun maki a Nijeriya. Saidai, JAMB ta ce bincike ya nuna cewa an sauya sakamakon nata ne da na bogin, tana…
Read More

Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawa ƙudirin gyaran dokar ilimin makarantun sakandare

Shugaba Bola Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa ƙudirin dokar gyaran Hukumar Kula da Manyan Makarantun Sakandare ta Ƙasa (NSSEC) na shekarar 2026, inda ya nemi da ta gaggauta amincewa da shi domin inganta tsarin gudanarwa da kula da manyan makarantun sakandaren gwamnati a Nijeriya. Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ne ya karanta wasiƙar a zauren majalisar, ranar Alhamis. Shugaba Tinubu ya bayyana cewa, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da ƙudirin tun a taronta na ranar 30 ga watan Afrilu, 2026, kafin Ma'aikatar Shari'a ta tantance tare da kammala shirya shi bisa tanadin doka. Shugaban ƙasar ya ce gyaran…
Read More

Shugaban alƙalai, Collina ya kare alƙalan wasan Kofin Duniya bayan ƙorafin Misra

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban alƙalan wasa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa-da-Ƙasa (FIFA), Pierluigi Collina ya yi tir da babban murya akan zarge-zargen Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Misra da Koci Hossam Hassan bayan Argentina ta yi nasara akan ƙasar da ci 3 da 2 a wasan zagayen 'yan 16 na gasar Kofin Duniya da ke cigaba da gudana a Nahiyar Amurka. Misra ta shigar da ƙara ne akan alƙalin wasa François Letexier a game da ƙwallon da aka soke da kuma hana 'yan wasanta buga fenareti yayin da ake gwabzawa tsakaninta da Argentina. "Lallai sun so su…
Read More

Ka kori wanda kake so bayan kafa gwamnatinka – Wike ga Atiku kan kiran tsige Gbajabiamila bisa badaƙalar hukumar bogi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Abuja Nyesom Wike, ya bayyana zarge-zargen da ake danganta wa Shugaban ma'aikatan Fadar Shugaban, Femi Gbajabiamila akan batun hukumar bogi ta PFIPC a matsayin siyasa. Wike ya bayyana haka ne a wata hira da 'yan jarida ta wata-wata a ranar Alhamis, inda ya yi watsi da dukkan wani yunƙuri na ɓata manyan masu taimaka wa Shugaba Bola Tinubu. Ministan ya kuma bayyana zargin Frins Adeniyi Adeyemi Matthew, wanda ya yi iƙirarin gudanar da PFIPC, akan Gbajabiamila a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama'a. A ɗaya gefen, Gbajabiamila ya fitar…
Read More

Na taɓa faɗa wa ‘yan bindiga su halaka ‘yan uwana akan na ba su kuɗin fansa, inji Gwamnan Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa yin sulhu da 'yan bindiga ba ko biyan su kuɗaɗen fansa don saboda sun yi garkuwa da mutane. Dauda Lawal ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi a taron manema labarai a game da al'amarin 'yan sandan jihohi, ranar Alhamis. A cewarsa, a shekarar 2019, an sace 'yan uwansa maza biyu, inda 'yan bindigar da ke da alhakin haka suka nemi a biya Naira miliyan 300 a matsayin kuɗin fansarsu. Ya ce, a madadin haka sai ya faɗa musu…
Read More

An musanta ƙorafi akan Sabo Nakudu da barazanar kai ƙara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar yaƙin naman zaɓe ta Mohammed Nakudu da Mallam Ibrahim Ringim ta jam’iyyar ADC ta yi watsi da ƙorafin da aka yi wa ɗan takarar gwamnanta na Jihar Jigawa, Sanata Sabo Nakudu, tana mai bayyana hakan a matsayin “cin fuska, ɓatanci da kuma makircin siyasa”. Rahotanni sun bayyana cewa, ƙungiyar ta ce wasu mutum biyu, wato Abubakar Sani da Ibrahim Mai Jama’a ne suka sanya wa ƙorafin hannu wadda aka fitar a ranar 7 ga Yuli, 2026, inda suka yi iƙirarin cewa su ‘yan ADC ne daga Ƙaramar Hukumar Gwaram da ke Jihar. A…
Read More

An yi wa shugabancin ADC ƙorafin Sanata Nakudu kan zargin da ICPC ta yi masa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu mambobin jam'iyyar ADC reshen Ƙaramar Hukumar Gwaram a Jihar Jigawa, sun yi wa shugabancin jam'iyyar na Ƙasa ƙorafin Sanata Sabo Nakudu da ke neman takarar gwamnan jihar bisa iƙirarin rashin cika alƙawuran ayyukan mazaɓa Daga ɓangarensa. Sun ce, Sanata Nakudu, wanda ya wakilci mazaɓar Jigawa ta Yamma daga shekarar 2015 zuwa 2023 na daga cikin waɗanda suka hana ruwa gudu a mazaɓar ta fuskar ayyukan ci-gaba da aka amince da aiwatar da su a hukumance. A wata wasiƙa da suka aike wa Shugaban ADC na Ƙasa da ke ɗauke da sanya hannun Abubakar…
Read More

An tsare lakcara a Katsina bayan zargin gwamnatin jihar da ɗaukar nauyin aikin hajjin wasu manyan ‘yan bindiga

Daga UMAR GARBA a Katsina Babbar Kotun Shari’a da ke Katsina ta ba da umarnin tsare Dr. Bashir Kurfi, malami a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, bayan rundunar ‘yan sandan Jihar ta gurfanar da shi bisa zargin vata suna da kuma yaxa bayanan qarya masu tayar da hankali kan gwamnatin jihar. Jaridar Daily Trust ta ruwaito ‘Yan sanda sun ce Dr. Kurfi ya yi iqirarin a wata hira da ya yi a Trust TV cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta xauki nauyin wasu ‘yan bindiga zuwa aikin Hajji, zargin da gwamnati ta musanta. Bayan ya musanta laifukan da ake tuhumarsa…
Read More