Babaji

4778 Posts

An tsare lakcara a Katsina bayan zargin gwamnatin jihar da ɗaukar nauyin aikin hajjin wasu manyan ‘yan bindiga

Daga UMAR GARBA a Katsina Babbar Kotun Shari’a da ke Katsina ta ba da umarnin tsare Dr. Bashir Kurfi, malami a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, bayan rundunar ‘yan sandan Jihar ta gurfanar da shi bisa zargin vata suna da kuma yaxa bayanan qarya masu tayar da hankali kan gwamnatin jihar. Jaridar Daily Trust ta ruwaito ‘Yan sanda sun ce Dr. Kurfi ya yi iqirarin a wata hira da ya yi a Trust TV cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta xauki nauyin wasu ‘yan bindiga zuwa aikin Hajji, zargin da gwamnati ta musanta. Bayan ya musanta laifukan da ake tuhumarsa…
Read More

Saboda wasu na neman rayuwata nake tunanin ba lallai a yi zaɓen 2027 Ina raye ba, inji Peter Obi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa akwai yiwuwar ba zai kasance a raye ba har zuwa zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027. Obi ya yi wannan furuci ne yayin wata hira da aka wallafa a shafin X na mai gabatar da shirye-shirye, Chude Jideonwo, inda ya zargi Gwamnatin Tarayya da hana shi gudanar da harkokinsa tare da matsa lamba akan 'yan adawa. Ya bayyana cewa, yana fuskantar cikas a kusan dukkan abubuwan da yake yi, inda ya yi zargin gwamnati na taka rawa wajen hana shi wasu hakkokinsa,…
Read More

An yi hayaniya yayin yunƙurin gayyatar Tinubu a Majalisar Wakilai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Zaman Majalisar Wakilai na ranar Laraba ya ɗauki wani ao bayan 'ya'yanta sun shiga halin tayar da jijiyan wuya akan shawarar neman gayyatar Shugaba Bola Tinubu ya je ya yi bayanin zargin jinkirta aiwatar da Dokar Kasafi ta 2025. Hakan ya biyo bayan da Ɗan majalisa Benedict Etanabene (Jihar Delta) ya yi tsokaci akan takardar umarnin da Akanta Janar na Ƙasa Shamseldeen Ogunjimi ya fitar. A takardar da aka umarci saƙonta ya fara aiki daga ranar 29 ga Yuni, an umarci baki ɗaya ma'aikatu, cibiyoyi da hukumomin tarayya da su dakatar da biyan kuɗaɗen…
Read More

Rikici ya ɓarke tsakanin Yarabawa da Hausawa a Ibadan kan kisan bakanike

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An shiga fargaba a yankin Ojo da ke cikin birnin Ibadan bayan wani rikici da ya ɓarke tsakanin mazauna Yarabawa da Hausawa a safiyar yau Laraba, 8 ga Yuni, 2026. An gano cewa, rikicin ya samo asalin ne sakamakon zargin kisan wani bayeraben bakaniken adaidaita sahu, wanda aka ce wasu 'yan bola jari Hausawa ne suka sassare shi da dare har ya rasu. Akan haka ne majiyoyi suka ce wasu matasa suka yi cincirindo a titina domin yin zanga-zanga akan zargin kisan bakaniken daga 'yan bolan, lamarin da ya tayar da rikici tsakanin ɓangarorin…
Read More

PSC ta kori manyan ‘yan sanda huɗu, ta rage wa 10 matsayi kan rashin ɗa’a

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da Harkokin 'Yan Sanda PSC, ta amince da sallamar wasu manyan jami'ai guda huɗu bisa ayyuka da dama da suka shafi rashin ɗa'a, a wani mataki na horo da nufin ƙarfafa tsare gaskiya, adalci da ƙwarewa a Hukumar 'Yan sandan Nijeriya. Babban Jami'in Hulɗa da jama'ar PSC, Torty Njoku Kalu ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Talata, bayan kammala zaman manyan jami'an PSC a hedikwatarta da ke Abuja. A cewar hukumar, an kuma rage wa wasu manyan jami'ai su 10 matsayi, yayin da aka ladabtar da…
Read More

Switzerland ta kai kwata fainal bayan doke Kolombiya a fenareti

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da ake cigaba da fafatawa a gasar Kofin Duniya na 2026, Ƙasar Switzerland ta yi nasarar kaiwa zagayen wasannin dab da na kusa da na ƙarshe bayan doke Kolombiya da ci 4 da 3 a bugun fenareti a zagayen 'yan 16. Da fari, an tashi wasan ne babu ci a tsakanin ɓangarorin biyu bayan shafe mintina 120 ana gumurzu a wasan mai cike da ɗaukar hankali. Luis Díaz na Bayern Munich ne kaɗai ya zubar wa Kolombiya fenareti, lamarin da ya ba Switzerland nasara a wasan. A yanzu, ƙasar za ta kara da…
Read More

Wanda ya yi silar ɗaukakar mu shine namu – Shugaban ƙungiyar ɗalibai

Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙaramar Hukumar Bichi ta gudanar da gagarumin taro a Sakatariyar ƙaramar hukumar domin jaddada aniyarta na cigaba da mara wa Ɗanmajalisar Tarayya mai Wakiltar Bichi, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar baya, domin cigaba da inganta ilimin al'ummar yankin, musamman yara da matasa a ƙaramar hukumar. A sanarwar da Jami'ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa manema labarai, Shugaban Ƙungiyar Ɗalibai na Bichi, Kwamared Mu'azzam Kabiru Adamu, ya bayyana gamsuwarsu ɗari bisa ɗari wajen mayar da alheri a gurbin alheri, dangane da irin yadda Ɗanmajalisar Tarayya na yankin ya jajirce na ganin kowane yaro…
Read More

Kano: Hanyoyi, tsaro da taki ne ginshiƙin bunƙasar noma, inji Sakataren Bichi

Sakataren Mulki na Ƙaramar Hukumar Bichi, Alhaji Anas Muhammad Abdullah,i ya ce, kula da ingancin hanyoyi da tsaro da kuma samar da taki ga manoma shi zai bunkasa harkokin noma. A sanarwar da Jami'ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, Sakataren ya bayyana hakan ne bayan ziyarar da Ma'aikatar Ayyuka ta Jihar Kano ta kai a ƙaramar hukumar bisa la'akari da irin ayyukan raya ƙasa da Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ke yi a ƙananan hukumomi 44 na jihar. Alhaji Anas, da ya yi magana a madadin Shugaban karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Maifata, ya bayyana…
Read More

Bayan bada umarnin bincike kan hukumar bogi, Tinubu ya ba Gbajabiamila sabon muƙami

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Talata Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar da kwamitin ƙasa na ayyukan kula da lamuran ƙudirin dokokin 'yan sanda, inda ya naɗa Shugaban ma'aikatan fadarsa, Femi Gbajabiamila a matsayin shugaba, a wani yanayi na nuna gamsuwa da aiki tare da shi yayin da ake cigaba da tirka-tirkar badaƙalar zargin gudanar hukumar bogi ta PFIPC. Haka kuma, a ranar ne Shugaba Tinubu ya umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da ta gudanar da gamsashshen bincike akan al'amarin "PFIPC". Shi ma Gbajabiamila a ranar hallau, ya yi barazanar shigar da ƙarar Naira…
Read More

Gwamnonin APC 18 masu wa’adin farko sun yi ganawar sirri a Kebbi

Gwamnoni guda 18 masu wa'adi na farko da aka zaɓa a ƙarƙashin jam'iyyar APC sun yi tir da hare-haren ƙyamar baƙi da ake kai wa 'yan Nijeriya a Afirka ta Kudu, inda suka bayyana hakan a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, tare da kira da a ƙara kare 'yan Nijeriya da ke zaune a ƙasashen waje. A cikin sanarwar bayan taron sirri da suka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar Kebbi a ranar Talata, gwamnonin sun tattauna akan batutuwan cikin gida da na ƙasa da ƙasa da suka shafi 'yan Najeriya. Gwamnonin sun bayyana goyon bayansu…
Read More