Babaji

4778 Posts

Yanzu-yanzu: Tinubu ya umarci a yi bincike kan hukumar bogi

A yau Talata Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da ta gudanar da cikakken bincike akan wata hukuma da ke kiran kanta Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), wadda ta yi iƙirarin cewa tana ƙarƙashin Fadar Shugaban Ƙasa ne. Umarnin ya biyo bayan gano cewa hukumar ba ta da wata doka ko sahalewar gwamnatin tarayya da ta kafa ta, kuma ba a taɓa amincewa da ita ta kowace hanya ba. Shugaban Ƙasar ya kuma ba ICPC wa'adin kwanaki 30 ta kammala binciken tare da miƙa masa cikakken rahoto. A cewar Fadar Shugaban Ƙasa,…
Read More

Kofin Duniya: Su Messi sun yi waje da Misra bayan farfaɗowa a zagayen ‘yan 16

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙasar Argentina ta yi nasara ana gab da tashi a wasa a karawarta da Misran su Mohammed Salah inda aka tashi 3 da 2 a zagayen 'yan 16 na gasar Kofin Duniya da ke cigaba da gudana a Nahiyar Amurka. Da fari dai Misra ce ta ja ragamar wasan bayan zura ƙwallo biyu a ragar Argentina, amma daga bisani zakaran ƙwallon ƙafa na Duniya Lionel Messi ya nuna bajinta yayin da wasan ya rage ƙasa da minti 20 a kammala. A minti na 15 ne Yasser Ibrahim ya samu damar zura ƙwallon farko da…
Read More

Badaƙalar PFIPC: Gbajabiamila ya yi barazanar shigar da ƙarar ɓatanci akan Adeyemi

Shugaban ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Femi Gbajabiamila, ya yi barazanar shigar da ƙarar ɓata suna ta Naira biliyan 10 akan Frins Adeniyi Adeyemi, bisa zarge-zargen da ya yi masa na hannu a kisan kai da kuma karɓar cin hanci. Lauyoyin Gbajabiamila sun bayyana cewa zarge-zargen da Adeyemi ya wallafa ta hanyar wata ƙungiya ƙarya ne, marasa tushe, kuma sun yi matuƙar ɓata masa suna da mutuncinsa. A cikin wasiƙar da aka aike wa Adeyemi, an buƙace shi da ya janye zarge-zargen nan take, ya goge dukkan wallafe-wallafen da ya yi, sannan ya wallafa cikakken uzuri a kafafen yaɗa labarai da…
Read More

An samu fashewar bom a kusa da wajen taron da Emmanuel Macron ya halarta a Siriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu ababen fashewa guda biyu sun tarwatse a birnin Damascus, inda Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya halarci wani zama a ranar Talata yayin da ya kai ziyara Siriya. A cewar Reuters, fashe-fashen sun faru ne a kusa da otal ɗin su Macron da ke babban birnin ƙasar, lamarin da ya tilasta wa hukumomin tsaro rufe hanyoyin zuwa yankin da ƙarfafa matakan tsaro. An ruwaito cewa, boma-boman sun fashe ne a wajen taruwar jama'a da ke tsakanin ma'aikatar walwalar Siriya da gidan adana kayan tarihi a sassan yankin da Macron ya gana da ƙungiyoyin al'umma.…
Read More

Kofin Duniya: Belgium ta yi waje da Amurka a zagayen ‘yan 16

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan wasa Folarin Balogun ya koma cikin tawagar 'yan wasan Amurka bayan Shugaba Donald Trump ya tsoma baki akan al'amarinsa na wasan da ya gabata. Saidai Balogun ya gaza taimaka wa ƙasar kai wa zagayen wasan dab da na kusa da na ƙarshe a karon farko tun a 2002 a gasar Kofin Duniyar da ke gudana a Nahiyar Amurka bayan da Belgium ta lallasa ta da ci 4 da 1. Tawagar Amurka ta fara gasar ne cike da ƙwarin-gwiwar kasancewarta a gida inda ta samu tikitin hayewa zagaye na gaba kai-tsaye daga na rukunin-rukuni.…
Read More

Mafarkin Ronaldo na lashe Kofin Duniya ya zo ƙarshe bayan Sifaniya ta doke Portugal a zagayen ‘yan 16

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan wasa Mikel Merino da aka sako daga baya ya yi nasarar zura ƙwallo a raga ana gab da kammala wasa inda aka tashi Sifaniya ta doke Portugal ta su Cristiano Ronaldo da ci 1 da 0 a gasar Kofin Duniya da ke cigaba da gudana a Nahiyar Amurka. Wannan al'amari ya kawo ƙarshen fatan zakaran ɗan ƙwallon duniya, Ronaldo zuwa ƙarshe bayan gumurzu da ƙasarsa a gasar har sau shida a tarihinsa. Haka kuma nasarar da Sifaniya ta samu dama ce ta cigaba da aiki tuƙuru wajen ganin ta lashe kofin a matsayinta…
Read More

PFIPC ba ta da asusu a CBN – Akanta Janar ya ci karo da Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A daiadai lokacin da 'yan Nijeriya ke cigaba da tsokaci akan badaƙalar hukumar bogi ta PFIPC, Ofishin Akanta Janar na Ƙasa (OACF) ya ce hukumar ba ta da asusun aiki a Babban Bankin Nijeriya (CBN), don haka ba a taɓa tura mata ko sisi daga kuɗaɗen gwamnati ba. Daraktan hulɗa da jama'a na ofishin a wata sanarwa, Bawa Mokwa, ya bayana cewa an dai fara yunƙurin buɗe asusun ne, amma ba a kai ga kammala shi ba saboda ba a cika wasu sharuɗɗa da ake buƙata ba. Ya ƙara da cewa, Adeniyi Adeyemi ya…
Read More

Badaƙalar PFIPC: AYCF ta nesanta kanta da kalaman goyon bayan Gbajabiamila

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Mashawartan Arewa na Matasa AYCF, ta nesanta kanta daga saƙon da aka wallafa da ke zargin ta fitar da wata sanarwa mai ƙunshe da goyon ga Shugaban ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila akan al'amarin hukumar bogi ta PFIPC. A wata sanarwa da ke ɗauke da sanya hannun Shugabanta, Alhaji Yerima Shettima a ranar Lahadi, AYCF ta musanta hannu a fitar da kowane saƙo akan al'amarin. A cewar sanarwar, wasiƙar da ake yaɗawa ba daga AYCF yake ba don haka al'umma su ƙaurace mata tare da saƙon da ke ciki. Sanarwar ta bayyana…
Read More

Kaduna: Hare-haren ‘yan bindiga sun yi ajalin manoma 9 da garkuwa da mutane da dama

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Asabar ne 'yan bindiga sun halaka kimanin manoma guda tara da kuma yin awon-gaba da wasu da dama a wasu hare-haren gonaki da ke a bayan garin ƙauyen Kakangi a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna. Rahotanni sun bayyana maharan sun buɗe wa manoman da ke aiki a gonakinsu wuta a lokacin da suka riske su suna bakin aiki, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum tara, kafin daga bisani suka tafi da wasu da ba a tantance adadinsu ba. Al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3 na yamma…
Read More

Sabbin bayanai sun alaƙanta ofishin sakataren gwamnati da daraktan hukumar bogi yayin da Majalisar Dattawa za ta yi zama akan kasafin biliyan N1.3

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An samu sababbin bayanai sun bjiro da ke nuna Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF) ya amince da Daraktan Hukumar Shugaban Ƙasa ta Ciyar da Lamuran Harkokin Waje Gaba (PFIPC) ta bogi, Mista Adeniyi Adeyemi, ya halarci Taron Canada-Africa Fintech (CAFS) a watan Agustan 2025. Wannan al'amari na zuwa ne a daidai lokacin da ake cece-kuce ciki har da allah-wadai daga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da kuma neman a bayyana haƙiƙanin gaskiyar al'amarin daga ɓangaren Cibiyar Tabbatar da Gaskiya da Adalci akan Albarkatun Ƙasa (SERAP) akan ware Naira biliyan 1.3 ga hukumar bogin…
Read More