
Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Femi Gbajabiamila, ya yi barazanar shigar da ƙarar ɓata suna ta Naira biliyan 10 akan Frins Adeniyi Adeyemi, bisa zarge-zargen da ya yi masa na hannu a kisan kai da kuma karɓar cin hanci.
Lauyoyin Gbajabiamila sun bayyana cewa zarge-zargen da Adeyemi ya wallafa ta hanyar wata ƙungiya ƙarya ne, marasa tushe, kuma sun yi matuƙar ɓata masa suna da mutuncinsa.
A cikin wasiƙar da aka aike wa Adeyemi, an buƙace shi da ya janye zarge-zargen nan take, ya goge dukkan wallafe-wallafen da ya yi, sannan ya wallafa cikakken uzuri a kafafen yaɗa labarai da kuma shafukan sada zumunta.
Gbajabiamila ya ce, matuƙar Adeyemi ya gaza bin waɗannan buƙatu cikin wa’adin da aka ba shi, zai fuskanci ƙarar neman diyyar Naira biliyan 10 saboda ɓata suna.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Adeyemi bai fitar da wata sanarwa ba a hukumance domin mayar da martani kan barazanar shigar da ƙarar tun bayan fara badaƙalar hukumar bogi ta PFIPC.
