Gobara ta yi sanadiyyar mutuwar yara biyu a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Gobara ta yi sanadiyyar mutuwar waɗansu yara biyu da dama kuma sun sami raunuka daban-daban a garin Yauri da ke jihar Kebbi daren jiya Lahadi.
Al-amin Ushe wani mazauni garin Yauri ya shaida wa waƙilin blueprint Manhaja da cewa gobarar ta tashi ne a gidan Alhaji Sanusi Bala Mai wake wani ɗan kasuwa da ke anguwar Illela ta kama da misalin ƙarfe goma na dare sanadiyyar wutar gawayi da ba a kashe da kyau ba bayan kammala girki.
Alhaji Sanusi bai magantu ba amma dai wani na kusa da shi ya bayyana cewa gobarar ta lalata dukiya ta milliyoyin kuɗi da ba a tantance adadin hasarar da aka yi ba yanzu.

By ukarofi

Leave a Reply