Tsaro na daga cikin manyan ginshiƙan da kowace al’umma ke dogaro da su wajen tabbatar da zaman lafiya, ci gaba da walwala. Duk inda aka samu ingantaccen tsaro, ana samun bunƙasar tattalin arziki, ilimi da sauran harkokin rayuwa. Haka kuma, duk inda tsarin tsaro ya samu nakasu, al’umma kan shiga cikin damuwa, fargaba da rashin tabbas.
Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ita ce babbar hukuma da aka ɗorawa nauyin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tabbatar da doka da oda, da kuma yaƙi da aikata laifuka. Duk da muhimmancin wannan hukuma, ba ɓoyayyen abu ba ne cewa tsawon shekaru al’umma sun daɗe suna kokawa kan wasu matsaloli da suke fuskanta daga hannun wasu jami’an ’yan sanda.
ɗaya daga cikin manyan matsalolin da suka fi damun jama’a shi ne batun karɓar rashawa. A kusan dukkan manyan hanyoyin Nijeriya, musamman a wasu wuraren binciken ababen hawa, ana yawan samun ƙorafe-ƙorafen cewa wasu jami’ai suna karɓar kuɗi daga direbobi da masu sana’ar kabu-kabu. Sau da yawa, matasa masu neman abin dogaro da kai ta hanyar aikin babur ko adaidaita sahu su ne ke fuskantar wannan matsala fiye da kowa. Wasu daga cikinsu kan yi ƙorafin cewa duk da wahalar rayuwa da tsadar man fetur, har yanzu suna fuskantar matsin lamba daga wasu jami’an tsaro da ke neman kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.
Wata matsalar kuma ita ce yadda a wasu lokuta ake samun zargin ƙulla wa marasa laifi sharri ko kama mutane ba tare da cikakken bincike ba. Akwai lokutan da mutum zai shiga wani hali saboda ƙarya ko zargin da ba a tabbatar da shi ba. Maimakon a gudanar da bincike mai zurfi domin gano gaskiya, sai a ga an kama mutum ko an tsare shi tsawon lokaci ba tare da hujja mai ƙarfi ba. Wannan lamari ya jawo wa mutane da dama asarar lokaci, kuɗi da kuma mutunci.
Haka kuma, al’umma sun sha yin ƙorafin cewa a wasu lokuta masu hannu da shuni ko masu tasiri sukan samu sauƙin kaucewa hukunci, yayin da talaka ke fuskantar tsauraran matakai. Wannan yanayi yana rage amincewar jama’a ga tsarin tabbatar da adalci. Domin babu abin da ke gina ƙasa kamar adalci, kuma babu abin da ke rusa amincewar jama’a kamar nuna bambanci wajen aiwatar da doka.
Sai dai duk da waɗannan ƙalubale, akwai alamu masu ƙarfi da ke nuna cewa ana samun gyara a Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya. A cikin watannin baya-bayan nan, an fara ganin sauye-sauye da dama da suka haɗa da ƙarfafa horo, ɗaukar matakan ladabtarwa kan jami’an da suka karya doka, da kuma ƙoƙarin kusantar da rundunar da jama’a.
ɗaya daga cikin mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen wannan yunƙuri shi ne Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Disu Rilwan. A ƙarƙashin jagorancinsa, an ga ƙarin mayar da hankali kan ladabtar da jami’an da suka aikata ba daidai ba, ƙarfafa bin ƙa’idojin aiki, da kuma ƙoƙarin dawo da martabar rundunar a idanun jama’a.
A lokuta da dama, rundunar ta nuna cewa ba za ta lamunci cin zarafin jama’a, karɓar rashawa, ko amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba. An samu rahotannin hukunta jami’ai da dama bayan bincike ya tabbatar da laifuffukan da ake zarginsu da aikatawa. Wannan wani muhimmin mataki ne da ke nuna cewa akwai niyyar gyara daga sama.
Haka kuma, ƙoƙarin amfani da fasaha wajen bincike da tattara bayanai yana daga cikin abubuwan da suka kamata a yaba. Yayin da duniya ke sauyawa, ya zama wajibi hukumomin tsaro su rungumi sabbin hanyoyin aiki domin magance matsalolin tsaro cikin sauri da inganci.
Wani muhimmin batu da ke ci gaba da jan hankali shi ne batun kafa ’yan sandan jihohi. Masu goyon bayan wannan ra’ayi suna ganin cewa kasancewar jami’an tsaro sun fi sanin yankunansu da al’adun mutanen da suke aiki tare da su zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro cikin sauri. Haka kuma, suna ganin hakan zai rage nauyin da ke kan Rundunar ’Yan Sandan Tarayya.
Sai dai akwai masu nuna damuwa cewa idan ba a gina tsarin da zai kare shi daga amfani da shi ta hanyar siyasa ba, wasu gwamnoni za su iya amfani da ’yan sandan jihohi wajen cimma manufofinsu. Don haka, duk wani yunƙuri na kafa ’yan sandan jihohi ya kamata ya kasance tare da cikakkun matakan kariya, doka mai ƙarfi da kuma tsarin sa ido mai zaman kansa.
Abin da ya fi muhimmanci shi ne a tabbatar da cewa ko wace irin rundunar tsaro ce, manufarta ita ce kare rayuka da dukiyoyin jama’a, ba tare da nuna bambanci ba. Dole ne jami’an tsaro su kasance masu biyayya ga doka da kundin tsarin mulki, ba ga son zuciyar mutum ko wata ƙungiya ba.
A yau, al’umma na son ganin rundunar da za ta kasance abar alfahari. Rundunar da talaka zai iya kai ƙorafinsa ba tare da tsoro ba. Rundunar da mai laifi zai ji tsoron ta saboda adalci da ƙwarewa, ba saboda zalunci ba. Rundunar da za ta kare marasa ƙarfi, ta hukunta masu laifi, kuma ta kasance abin koyi ga sauran hukumomin gwamnati.
Saboda haka, akwai buƙatar a ci gaba da gyare-gyaren da aka fara. Ya kamata a ƙara horar da jami’ai, a inganta albashinsu da walwalarsu, a samar musu da kayan aiki na zamani, sannan a tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifin cin hanci, cin zarafi ko take haƙƙin jama’a ya fuskanci hukunci ba tare da la’akari da matsayinsa ba.
Hakazalika, jama’a ma suna da rawar da za su taka. Bai kamata a ci gaba da ba jami’ai cin hanci ba domin kaucewa doka. Ya kamata kowa ya taimaka wajen samar da bayanan sirri da za su taimaka wa hukumomin tsaro wajen yaƙar masu aikata laifuka.
A ƙarshe, duk da ƙalubalen da suka daɗe suna addabar Rundunar ’Yan Sandan Nujeriya, akwai alamun da ke nuna cewa ana tafiya a hanyar gyara. Wannan gyara yana buƙatar haɗin kan gwamnati, shugabannin rundunar, jami’ai da kuma jama’a baki ɗaya. Idan aka ci gaba da tafiya a wannan hanya ta gaskiya, adalci da ƙwarewa, babu shakka za a samu rundunar ’yan sanda da za ta kasance abin alfahari ga Nijeriya da ’yan Nijeriya.
Lallai akwai fa gyara a rundunar ’yan sanda, amma wajibi ne a tabbatar da cewa wannan gyara ya kai har ƙasan tsarin aiki, domin kowane ɗan ƙasa ya ji daɗin adalci, tsaro da mutunta haƙƙinsa a ko’ina cikin ƙasar nan.
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD. 07066778190.
