Daga ABUBAKAR TUKUR IBRAHIM
Korafe-ƙorafen da ake yi dangane da Tashar Samar da Wutar Iska ta Lambar Rimi abu ne da ya dace, domin kowane ɗan Jihar Katsina na son ganin injinan samar da wutar sun fara aiki tare da isar da wutar lantarki zuwa gidaje, wuraren kasuwanci, masana’antu da sauran al’ummomi.
Sai dai, yayin da ake ci gaba da bayyana damuwa kan jinkirin aikin, yana da muhimmanci a fayyace ainihin matakan da aka ɗauka a ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, domin ceto aikin daga halin da ya tsinci kansa tare da sanya shi kan turbar kammalawa.
Lokacin da Gwamna Radda ya karɓi ragamar mulki a shekarar 2023, ya tarar da aikin cikin mawuyacin hali. Tashar ba mallakin Gwamnatin Jihar Katsina ba ce, domin tana ƙarƙashin Gwamnatin Tarayya. Haka kuma, ta fuskanci matsaloli da suka haɗa da lalacewar fasaha, rashin kammala gwaje-gwajen ƙarshe, rashin tabbas kan mallaka da kuma rashin tsarin gudanarwa mai ɗorewa.
Duk da cewa an daɗe ana magana kan aikin, Gwamna Radda ya zaɓi ɗaukar matakin da ya dace maimakon ci gaba da yin magana kawai.
Yayin da yake fahimtar muhimmancin tashar ga ci gaban jihar, gwamnan ya jagoranci tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da Ma’aikatar Wutar Lantarki ta Tarayya, Hukumar Kula da Kasuwancin Kadarorin Gwamnati (BPE), Hukumar Kula da Yarjejeniyar Zuba Jari ta Ababen More Rayuwa (ICRC), Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO), da kuma kamfanin ɓergnet na ƙasar Faransa wanda ya samar da kayayyakin aikin.
A wani yunƙuri na musamman, Gwamna Radda ya kai ziyara zuwa ƙasar Faransa inda ya gana da shugabannin kamfanin ɓergnet. A yayin ziyarar, ya duba fasahar da ake amfani da ita, ya tattauna da ƙwararru tare da nemo hanyoyin da za su taimaka wajen gyara da kammala aikin.
Wannan mataki ya haifar da gudanar da cikakken binciken fasaha kan injinan samar da wutar lantarki guda 37 da ke tashar. Binciken ya tantance matsalolin da kowanne injin ke fuskanta, hanyoyin gyaransu da kuma kuɗaɗen da ake buƙata domin dawo da su aiki yadda ya kamata.
Baya ga hakan, gwamnatin jihar ta shirya tare da gabatar da Takardar Tsarin Kasuwanci (Outline Business Case – OBC) ga Hukumar ICRC domin samar da hanyar miƙa aikin, kammala shi da kuma tabbatar da dorewar gudanar da shi a nan gaba.
Rahotanni sun nuna cewa wannan takarda ta samu amincewa daga hukumomin da abin ya shafa, ciki har da Ma’aikatar Wutar Lantarki ta Tarayya, ICRC da BPE. Hakan ya sa aka ba da shawarar miƙa tashar ga Gwamnatin Jihar Katsina saboda ƙwarin gwiwa da shirye-shiryen da ta nuna wajen kammala aikin.
Har ila yau, gwamnatin jihar ba ta tsaya kan gyaran tashar kaɗai ba. Ta kuma tsara yadda za a haɗa samar da wutar iska da tsarin hasken rana da kuma na’urorin adana makamashi, domin tabbatar da samar da wutar lantarki mai ɗorewa da inganci ga al’ummar jihar.
Bugu da ƙari, gwamnatin ta ɗauki wasu matakai na bunƙasa fannin makamashi da suka haɗa da samar da ƙananan tashoshin hasken rana, samar da tsarin hasken rana a asibitoci, makarantu da cibiyoyin gwamnati, da kuma faɗaɗa ayyukan samar da wutar lantarki a yankunan karkara.
Waɗannan matakai ba alkawura ba ne kawai, ayyuka ne da ake iya gani da auna sakamakonsu.
Tabbas, al’ummar Katsina na da haƙƙin tambayar lokacin da za a kammala aikin. Sai dai kammala irin wannan babban aiki na buƙatar bin matakan fasaha, na shari’a da na gudanarwa domin tabbatar da dorewar sakamakonsa.
Abin da ya fi muhimmanci shi ne cewa, a karon farko cikin shekaru masu yawa, an samu cikakken binciken fasaha, an tsara hanyoyin gyara, an samu goyon bayan hukumomin da abin ya shafa, sannan an samar da tsarin da zai tabbatar da ci gaba da gudanar da aikin bayan kammalawa.
Wannan ci gaba bai zo da kansa ba. Ya samo asali ne daga ƙuduri da jajircewar Gwamna Dikko Umaru Radda na ganin cewa Tashar Wutar Iska ta Lambar Rimi ba ta ci gaba da kasancewa alamar damar da aka rasa ba, sai dai ta zama ginshiƙi na ci gaban tattalin arziki da samar da makamashi a Jihar Katsina.
Tafiyar ba ta kai ƙarshe ba tukuna, amma a yau ana iya cewa an fara hango ƙarshen tafiyar a sarari. Gwamna Radda bai gaji matsalar ba, amma ya ɗauki alhakin warware ta. Wannan shi ne abin da ake kira shugabanci mai hangen nesa da ɗaukar nauyi.
