Hikimomi a ilimi

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ

Tashin farko sai Allah ya ce mana “Iqra’a”, wato karatu shine ginshikin ilimi gaba dayansa, da zarar an sami damar karatu, to babu abinda zai biyo baya sai kuma rubutu. Amma fa shi rubutu ba ya kure karatu domin ba sai da rubutu ake iya karatu kawai ba. Shi yasa Allah ya ce mana “Da tekunan duniya zasu zama tawada, bishiyoyi kuma su zama alkaluma, ba za’a iya rubuce ilimin kalmomin ubangiji ba.”

Asalin Ilimi kuma ya faro ne daga wahayi lokacin da Allah ya yi wahayi ga Habila da Kabila su bada baiko. Kabila, manomi ya bada hatsi, shi kuma Habila makiyayi ya bada dabba. Sakamakon karbar baikon Habila ya sa kishi ya jefa Kabila halaka, domin ya kashe ɗan uwansa.

Bayan kisan sai ya rasa inda zai yi da gawar, saboda Dan Adam na zaune a duhu bai san komai ba sai abinda aka sanar da shi. To a wannan gaba kuma sai Allah ya samar masa wata sabuwar hanyar ta samun ilimi, wato ta Ilhama, wato yadda Allah ke saka wani ilimi kai tsaye cikin kwakwalwar mutum. Sai hankaka ya zo ya na hakar rami a kusa da gawa, abinda ya baiwa Kabila ilhamar ya tona rami ya binne gawar.

Ta hanyar ilhamar dai Allah ya koyawa Nuhu yadda zai gina jirgin ruwa, hanyar sufuri ta farko a tarihin dan Adam. Sakamakon da ya fara baiwa dan Adam damar fantsama daga nahiyar Afirka zuwa ga wasu nahiyoyin a bayan kasa bayan án gama ruwan dufana.

Mutanen Salihu ne suka fara kiwo da rakumi, abinda ya kara baiwa dan Adam damar habaka wata sabuwar hanyar sufuri da samun abinci. Mutanen Madayana suka samar da hanyar ciniki, ta hanyar musaya (barter).

Annabi Ibrahim ya zo ya fara kokarin gane wanene ya halicci komai kuma menene ya cancanci a bautawa saboda bai gamsu da cewa a bautawa gunkin da ka sassaka da kan ka ba. Sai ya fara nazarin taurari a wajen kokarinsa na gane wanene mahalicci. Amma bai gamsu da bautawa rana, wata ko taurari ba domin babu tabbatacce a cikinsu.

Annabi Ibrahim ne ya fara nazari ta hanyar falsafanci, domin tun yana tallan gumaka wani yazo siya sai ya ce masa “Shekarar ka nawa?” Ya ce “Hamsin” sai ya ce “Amma za ka sayi gunkin da aka sassaka jiya-jiya?”

Sannan lokacin da ya karya gumaka aka rutsa shi kan sai ya fadi wanda yayi aika-aikar, sai ya ce a tambayi babbansu. Sannan kuma a muhawarsa da Lamarudu da ya ce shi ma Allah ne sai ya ce to “Allah na, shine wanda ke fito da rana daga gabas zuwa yamma, kai kuma ka fito da taka daga yamma mana”. Wannan shine tsarin falsafanci, wato amfani da fikira (logic) domin tabbatarwa ko kore wani abu cikin hikima da basira.

Baban namu Ibrahima dai shi ya fara ilimin kimiyya lokacin da ya tambayi Allah yadda yake samar da rayayye daga matacce. Allah ya ce yayi gwajin kimiyya (eɗperiment) da tsuntsaye hudu.

Ta hanyar Annabi Musa kuma muka sami ilimin badini wanda ta hanyar sufanci ake tsinkayarsa. Cikakken labarin na nan a suratul Kahfi inda Musa ya tafi wajen babban Sufi, Halliru, wanda ya yi masa tarbiyya ta ilimin badini (esoteric). Annabi Yusuf ya zo mana da ilimi psychoanalysis ta hanyar fassara mafarki, sannan ya kara mana da ilimin tattalin arziki. Annabi Isa ya zo da ilimin warakar cutuka (medicine).

Annabin ƙarshe, Muhammdu Rasulilillah, cikamakin annabawa kuma cikamakin ilimi. Ilimin da ya zo da shi cikin Qurani shine ya baiwa musulman farko damar kafa ginshikin kimiyya da ilimin zamani. Musulmi suka fara kirkirar naurar sufuri ta zamani, Astrolabe, kyamarar daukan hoto, gilashin hangen sararin samaniya, kayan fidar mutum, jirgin sama na farko, inji mai amfani fa ruwa, naurar sanyaya waje, naurar kidaya, ginshikin kwamfuta da sauran abubuwa da dama.

Bahaushe na cewa “Ilimi kogi ne” don haka, duk iya nutson ka, saidai kayi bundum-bundum a iya inda kake, kuma shi ilimi ná Dan Adam gaba daya kamar ginin benaye ne. A hankali a hankali, al’ummomi daban daban ke habaka shi. A tsarin duniya ba imani ne ke baiwa mutane nasarar ci gaba ba, illa dai ilimi. Shi yasa tun asalin Dan Adam zuwa yanzu, kuma har karshen duniya, duk al’ummar da ta rungumi ilimi da nazari da bincike zaka samu ita ce jagorar zamaninta. Idan ta yi watsi da ilimi, duk wadda ta maye gurbinta a fagen, ita za ta zama jagora.

Wannan ne ya sa a bayan zuwan musulunci musulmi su ka zama gagara badau a fannonin ilimi yadda Daulolin Bagadaza da Andalus suka mulki duniya. Amma musulmi na kwanciya barci sai makwabtansu, turawa, suka karbe ilimi. Ko a zamaninmu munga yadda Turai, da su ka maye gurbin Musulmi a ilimi, sai aka wayi gari Amurka ta kwace daga hannunsu, a yanzu kuma China na kokarin kwacewa daga Amurka, yanda nan da yan shekaru kalilan zasu karbi gaba. Domin a yanzu sun zarce Amurka a fannoni da dama na bincike a fasaha.

Shi yasa Allah ya ce mana ko tekuna sun zama tawada, bishiyoyi sun zama alkaluma ba zamu iya kurewa ilimi gudu ba. Amma dai mu sani cewa kalubalenmu a kullum shine tsayawa kan “Iqra’a”, wato a yi ta karatu da nazari da bincike, sannan kada mu manta da addu’ar Manzo da ya ke cewa a cikin Qurani “Rabbi zidni ilma”.

Ranar da musulmi su ka dawo kan wannan turba, wato ta fifita ilimi a doron nazari da bincike, watakila idan hakan ta samu, zasu iya dawowa su mulki duniya a karo na biyu.
Amma dan uwa, kafin wannan mafarkin ya tabbata, yi kokari ka yi karatu da nazari da bincike domin samun damar ka iya mulkar naka tunanin.

By ukarofi

Leave a Reply