Daga AHMID LAWAL a Abuja
Kotun ɗaukaka ƙara ta shiyyar Owerri ta tabbatar da cewa shugabancin Jam’iyyar Labour Party na ƙasa ne kawai, ƙarƙashin Sanata Nenadi Usman, ne zai iya ba da izinin shigar da ƙara a madadin jam’iyyar.
Wannan na cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar Labour Party na ƙasa, Ken Asogwa, ya fitar a Abuja ranar Litinin. Ya ce hukuncin ranar 2 ga Yuli na kotun ɗaukaka ƙara, shiyyar Owerri, a cikin ƙarar lamba CA/OW/104/2026: Labour Party da 14 wasu da sauransu v. Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Abia da wasu huɗu ya sake tabbatar da ikon shugabancin da Usman ke jagoranta na shigar da ƙara ko kare jam’iyya a kotu.
A cewarsa, an shigar da wannan ɗaukaka ne saboda rigimar da ta taso kafin zaɓe bayan jam’iyyar ta gano cewa an shigar da ɗaukaka ƙara a madadinta ba tare da sanin, amincewa ko izinin shugabancin ƙasa na halal ba.
Ya ce mai ba da shawarar shari’a na jam’iyyar na ƙasa, Mrs Taiwo Ajayi, daga baya ta ba Mr C. Okoroafor umarni ta hanyar wasiƙa mai kwanan wata 22 ga Yuni, 2026, ya wakilci Labour Party ya ɗauki matakan da suka dace na janyewa daga ƙarar.
Ya ƙara bayani cewa, da aka kawo ƙarar a gaban kotun ɗaukaka ƙara, lauyoyi biyu ne suka bayyana suna wakilcin Labour Party. Wannan ya sa kotun ta nemi hujjar rubutu da ke nuna cewa suna da hurumi na wakilcin jam’iyyar.
Jam’iyyar ta ce yayin da Mrs A. Oteh ta dogara da wasiƙa daga Mr Ceekay Igara wanda ya ce shi ne mataimakin shugaban jam’iyya na yankin Kudu maso Gabas, Okoroafor ya gabatar da wasiƙar izini da mai ba da shawarar shari’a ta ƙasa ta bayar a madadin shugabancin ƙasa na halal.
Kotun ta amince da izinin da aka bayar ta ofishin mai na da shawar shari’a na ƙasa a matsayin ingantaccen izini. Bayan haka Oteh ta janye halartar ta da kuma bayanin tsayawa da ta shigar a ƙarar.
Daga bisani kotun ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar kuma ta yanke hukuncin biyan Naira 100,000 na tara lauya da ya yi aiki bisa izinin Igara.
”Jam’iyyar ta ɗauki wannan hukunci a matsayin muhimmi, domin ya sake tabbatar da ƙa’idar doka da aka saɓa cewa shugabancin ƙasa na halal ne kawai, ta hannun jami’ansa masu izini, ke da hurumin doka na ɗaukan lauya da kuma shigarwa, karewa ko ci gaba da shari’a a madadin Labour Party.
”Haka kuma, wannan hukunci ya sake tabbatar da Sanata Nenadi Usman a matsayin shugaba ɗaya tilo na halal kuma sahihiyar jam’iyyar. Jam’iyyar ta kuma yi alƙawarin ci gaba da nuna adawa ga yunƙurin mutanen da ba su da izini na yin aiki a madadinta.
”Labour Party ta sake jaddada cewa za ta ci gaba da ƙalubalantar kowane yunƙuri na mutanen da ba su da izini, ciki har da Julius Abure da Mr Ceekay Igara, na cewa su wakilai ne na Labour Party ko kuma su shigar, kare ko ci gaba da shari’a a madadinta ba tare da izini na doka ba,” in ji Asogwa.
A nasa martani ga hukuncin a ranar Litinin, Kakakin ƙungiyar Julius Abure ta jam’iyyar, Obiora Ifoh, ya ce ba su gamsu da hukuncin ba amma za su ƙalubalanci shi a kotun ƙoli.
Yayin da ya ce Abure zai bi umarnin kotun, Ifoh ya ce nan take za su tafi ƙotun ƙoli domin ƙalubalantar hukuncin.
Rigima kan shugabancin Labour Party ta kasance batun ƙararraki da dama a kotu sakamakon ikirarin ɓangarori biyu kan shugabancin jam’iyya na ƙasa, inda kwamitin zartarwa ƙarƙashin Nenadi ya lashe yawancin ƙararrakin.
