Akanza ya yabi Tinubu da Gwamna Sule kan ayyukan hanyoyi

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Lafia

Shugaban yankin raya Lafia ta Arewa Hon. Nasiru Kasimu Akanza ya yaba wa shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa bisa ayyukan hanyoyi da ake cigaba da yi, yana mai cewa ayyuka ne na tarihi da za su inganta cigaban tattalin arziki da sauƙaƙe zirga-zirga a faɗin ƙasa.

Da yake tattaunawa da manema labarai a ofishinsa da ke Shabu na ƙaramar hukumar Lafia, Akanza ya yaba da ƙaddamar da aikin babbar hanyar Akwanga zuwa Jos da Gombe da Maiduguri da kuma buɗe hanyar kilomita 3 mai layi biyu da aka gina a Akwanga da sauran su.

A cewarsa waɗannan ayyuka za su rage cunkoson motoci da inganta tsaron hanya da sauƙaƙe zirga-zirgar mutane da kaya da kuma bunƙasa harkokin tattalin arziki da zamantakewa a jihar ta Nasarawa da kewaye.

Ya kuma yabi shirin cigaban ababen more rayuwa na Gwamna Sule yana mai bayyana shi a matsayin gado mai amfani ga tsararraki masu zuwa.

Shugaban yankin rayawar Hon. Nasiru Kasimu Akanza ya kuma buƙaci al’ummar jihar da su cigaba da bai wa gwamnatin Gwamna Sule goyon baya yana mai cewa ayyukan cigabansa sun ba shugabannin ƙananan hukumomi da masu gudanarwa na yankuna ƙwazo wajen kawo ayyukan cigaba a matakin ƙasa.

Akanza ya yaba wa hukumomin tsaro bisa ƙokarinsu na daƙile laifuka yana mai cewa yanayin tsaro a Lafia da yankunan dake kewaye da ita ya inganta sosai.

“Ina son in tabbatar muku cewa yanzu muna jin daɗin zaman lafiya a Shabu da al’ummomin da ke kewaye da ita idan aka kwatanta da da. Tun da na hau kujera a matsayin shugaban yankin rayawar nan na Lafia ta Arewa na tattauna da jami’an tsaro domin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da laifuka kuma sakamako yana da kyau. A yau mutane na iya yin sana’o’insu cikin lumana ba tare da tsoron masu laifi ba,” in ji shi.

Akanza ya kuma yi kira ga matasan jihar Nasarawa dasu guji tashin hankali kada su bari ‘yan siyasa masu son kai su yi amfani da su yayin da ake shirin zaɓen 2027.

Ya buƙaci matasa da su kasance masu biyayya ga doka su kuma inganta zaman lafiya tare da kuma ba da gudummawa ga cigaban jihar.

“Dole ne mu kasance faɗake mu guji ‘yan siyasar da ke son amfani da matasa don biyan buƙatunsu. Maimakon mu zama masu lalata, ya kamata mu haɗa kai wajen kare al’ummominmu da inganta zaman lafiya. Gwamna Abdullahi Sule shugaba ne mai son zaman lafiya ya kamata mu yi koyi da jajircewarsa kan haɗin kai da cigaba,” in ji shi.

Shugaban a ƙarshe sai ya jaddada aniyar gwamnatinsa na cigaba da bai wa hukumomin tsaro goyon baya don aiwatar da manufofin da za su inganta zaman lafiya da tsaro da cigaba mai ɗorewa a faɗin yankin rayawar ta Lafia ta Arewar baki ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply