06
Jul
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Asabar ne 'yan bindiga sun halaka kimanin manoma guda tara da kuma yin awon-gaba da wasu da dama a wasu hare-haren gonaki da ke a bayan garin ƙauyen Kakangi a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna. Rahotanni sun bayyana maharan sun buɗe wa manoman da ke aiki a gonakinsu wuta a lokacin da suka riske su suna bakin aiki, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum tara, kafin daga bisani suka tafi da wasu da ba a tantance adadinsu ba. Al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3 na yamma…
