05
Jul
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore ya ce gwamnatin ƙasar za ta bibiyi tare da sanya ido a babban zaɓen Nijeriya na 2027, yana mai cewa shi da Shugaba Donald Trump za su kasance masu kula da yadda za a gudanar da zaɓen. Moore, wanda ɗan jam'iyyar Republican da ke wakiltar Virginia ta Yamma ne, ya bayyana haka ne a wata hira ta gidan talabijin na Noire a rana Lahadi a lokacin da yake amsa tambayoyi akan zaɓen Nijeriya da ke tafe. A cewarsa, Washington za ta kula sosai da hanyoyin da za bi…
