
Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari a garin Geidam da ke Ƙaramar Hukumar Geidam t Jihar Yobe, inda suka ƙone motoci huɗu, ciki har da babbar mota da ke ɗauke da kayayyakin ‘yan kasuwa na miliyoyin Naira.
Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:30 na safiyar Juma’a yayin da al’umma ke shirin gudanar da sallar asubahi.
Maharan sun fara kai hari sakatariyar ƙaramar hukumar inda suka ƙone motar Toyota Hilux da wata motar bus mallakin ƙaramar hukumar, kafin daga bisani su ƙone wata babbar mota da ke ɗauke da kayan ‘yan kasuwa da kuma wata mota da aka ajiye a kasuwa.
Rahotanni sun ce ‘yan kasuwar sun loda kayansu tun cikin dare suna jiran gari ya waye kafin su kama hanya, sai dai maharan suka banka wa motar wuta tare da dukkan kayayyakin da ke cikinta.
Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun shiga garin ne a ƙafa bayan sun bar baburansu a wajen gari. Duk da haka, babu rahoton asarar rai ko jikkata sakamakon harin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce yankin na ƙarƙashin kulawar sojoji.
