Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shirin Raya ƙasashe na Majalisar ɗinkin Duniya (UNDP) tare da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da sauran masu ruwa da tsaki sun yi kira da a gaggauta kawar da matsalolin kuɗi, na iyakoki da sauran ƙalubalen da ke hana mata gudanar da kasuwanci cikin sauƙi a nahiyar Afirka, suna masu gargaɗin cewa ci gaba da ware mata daga cikakken shiga harkokin kasuwanci na iya jefa kasuwar bai ɗaya ta nahiyar da darajarta ta kai dala tiriliyan 3.4 cikin haɗari.
An bayyana wannan ne a yayin taron yanki na HerAfCFTA 2026 da aka gudanar a Abuja ƙarƙashin inuwar Yarjejeniyar Kasuwanci Cikin ’Yanci ta Nahiyar Afirka (AfCFTA), mai taken “Mata Na Jagorantar Sauyin Tattalin Arzikin Afirka Ta Hanyar Kasuwancin Cikin Nahiyar: Faɗaɗa Tasiri.”
Taron ya haɗa ministoci, kwamishinonin kasuwanci, abokan hulɗar ci gaba, shugabannin masana’antu da ’yan kasuwa mata daga sassa daban-daban na Afirka. Masana da mahalarta taron sun yi gargaɗin cewa burin Afirka na samar da mafi girman kasuwa bai ɗaya a duniya ba zai cika ba matuƙar gwamnatoci ba su ɗauki matakan gaggawa wajen cire shingayen da ke hana mata ’yan kasuwa da masu safarar kayayyaki samun cikakken damar cin gajiyar kasuwancin nahiyar ba.
Yayin da take jawabi a taron, Mataimakiyar Sakatare Janar ta Majalisar ɗinkin Duniya kuma Daraktar Ofishin UNDP na Nahiyar Afirka, Ahunna Eziakonwa, ta ce mata su ne ginshiƙin tattalin arzikin ƙananan sana’o’i da kasuwancin da ba su cikin tsarin hukuma a Afirka, amma har yanzu ba su da isasshen damar cin gajiyar manufofi, tallafin kuɗi da ababen more rayuwa da za su taimaka musu wajen faɗaɗa kasuwancinsu a faɗin nahiyar.
Ta nuna damuwa cewa duniya na fuskantar matsalolin katsewar hanyoyin samar da kayayyaki, ƙaruwa da kariyar tattalin arziki da kuma raunin haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, lamarin da ya sa ya zama wajibi Afirka ta dogara da kanta wajen bunƙasa ci gabanta.
A cewarta, yarjejeniyar AfCFTA wata muhimmiyar hanya ce da za ta taimaka wa Afirka ta riƙe ƙimar albarkatunta, ta gina hanyoyin samar da kayayyaki masu ɗorewa tare da rage dogaro da fitar da albarkatun ƙasa ba tare da sarrafa su ba.
Eziakonwa ta buƙaci gwamnatocin Afirka su daidaita dokoki da ƙa’idojin kasuwanci, su sauƙaƙa hanyoyin kwastam, su zamanantar da hanyoyin sufuri da dabarun jigilar kayayyaki, su samar da tsarin biyan kuɗi na zamani da zai iya aiki a ƙasashe daban-daban, tare da kawar da duk wata matsala da ke hana zirga-zirgar kayayyaki da ayyuka cikin sauƙi a nahiyar.
Ta ce, “A lokacin da wasu yankuna ke rarrabuwa, Afirka na zaɓar haɗin kai. A lokacin da wasu ke gina katanga, Afirka na gina gadoji. Idan mata ba za su iya cin gajiyar kasuwar AfCFTA ba, to Afirka ta gina kasuwa ne domin rabin al’ummarta kawai.”
Ta kuma yi kira da a aiwatar da sauye-sauye cikin gaggawa, ciki har da sauƙaƙa dokoki ga mata masu kasuwanci, ƙara saka hannun jari a ababen more rayuwa da tsarin dijital, da kuma tabbatar da mata sun samu wakilci a tattaunawar kasuwanci da tsara manufofi.
