Farashin gas ya fara sauka bayan wadatarsa a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Al’ummomi a sassa daban-daban na Nijeriya sun fara samun sassauci kan farashin gas na girki, bayan da farashin iskar gas mai ruwa (LPG) ya fara raguwa sakamakon ƙarin wadatar kayayyakin da kuma saukar farashin saye daga manyan cibiyoyi.

Rahoton kasuwa na baya-bayan nan daga masu kasuwancin gas ya nuna cewa farashin gas na girki ya fara sauka a manyan biranen ƙasar nan bayan makonni da aka shafe ana fama da tsadar sa. Sai dai raguwar farashin ba ta zo daidai a ko ina ba, saboda bambancin kuɗin sufuri, nisan wuraren ajiya da kuma ribar da dillalai ke ɗorawa.

Binciken da masu kasuwancin suka gudanar ya nuna cewa a yanzu ana sayar da gas tsakanin naira 1,100 zuwa 1,350 kan kowanne kilogram a biranen Legas, Ibadan da Abeokuta. A biranen Benin, Fatakwal da Warri kuwa, farashin yana tsakanin naira 1,150 zuwa 1,400 kan kilogram.

A Onitsha da Enugu kuma, farashin yana tsakanin naira 1,200 zuwa 1,450 kan kilogram, yayin da mazauna Abuja ke sayen gas tsakanin naira 1,250 zuwa 1,500 kan kilogram.

Shugaban ƙungiyar Masu Kasuwancin Iskar Gas Ta Nijeriya (NALPGAM), Mista Edu Inyang, ya bayyana cewa biranen Kano da Kaduna na da farashin tsakanin naira 1,300 zuwa 1,550 kan kilogiram, yayin da Maiduguri da wasu yankunan Arewa maso Gabas ke ci gaba da fuskantar mafi tsadar farashi, tsakanin naira 1,350 zuwa 1,650 kan kilogram, saboda tsadar jigilar kayayyakin zuwa yankin.

A cewarsa, matsakaicin farashin gas a faɗin Nijeriya yanzu yana tsakanin naira 1,100 zuwa 1,650 kan kilogiram, duk da cewa wasu ƙananan dillalai a unguwanni har yanzu suna sayarwa sama da wannan farashi saboda tsadar harkokin rarrabawa.

Wannan sauyin ya zo ne bayan hauhawar farashi da aka gani tun daga watan Mayu, lokacin da ƙarancin kayayyaki da tashin farashin a manyan cibiyoyin ajiya suka haddasa tsadar gas a yankuna da dama na ƙasar.

Shugaban NALPGAM ya danganta raguwar farashin da ƙarin wadatar kayayyaki daga masana’antun cikin gida da kuma shigo da gas daga ƙasashen waje. Haka kuma ya ce raguwar farashin a cibiyoyin ajiya da ƙarin gasa tsakanin masu kasuwanci sun taimaka wajen kawo sauƙin.

Ya ce, rahotanni sun nuna cewa wadatar gas ta inganta sosai a ƙarshen watan Yuni na shekarar 2026, lamarin da ya sa farashin ya fara sauka a wasu kasuwanni. Sai dai ya jaddada cewa bambancin kuɗin sufuri da nisan wuraren ajiya na ci gaba da haifar da bambancin farashi tsakanin birane.

Masana harkar sun bayyana cewa wannan ci gaba zai taimaka wa gidaje da dama da ke fama da tsadar rayuwa, ko da yake har yanzu ana sa ran farashi zai ci gaba da bambanta daga yanki zuwa yanki.

Bisa ga farashin da ake samu a yanzu, cika tukunyar gas mai nauyin kilo 5 zai kai tsakanin naira 5,500 zuwa 8,250, yayin da cika ta kilo 6 zai kai tsakanin naira 6,600 zuwa 9,900. Haka kuma cika tukunyar kilo 12.5 zai kai tsakanin naira 13,750 zuwa 20,625, gwargwadon wurin da aka saya da kuma dillalin da ake hulɗa da shi.

Duk da wannan sauƙi, masu kasuwanci sun ce har yanzu ba a kai ga daidaiton farashi gaba ɗaya a faɗin ƙasar ba. Sun yi nuni da cewa yankunan da ke nesa da manyan cibiyoyin adana gas za su iya ci gaba da fuskantar tsadar farashi saboda ƙalubalen sufuri.

Masu ruwa da tsaki a harkar sun nuna kwarin gwiwa cewa idan wadatar gas daga masana’antun cikin gida da kuma shigo da ita daga waje ta ci gaba ba tare da tangarda ba, farashin zai ƙara sauka a makonni masu zuwa.

Shi ma Shugaban Reshen Dillalan Gas na ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas Ta Najeriya (NUPENG), Ayobami Olarinoye, ya ce sannu a hankali harkar na komawa yadda take a baya.

Sai dai ya bayyana cewa membobinsu da ke gudanar da ƙananan shagunan sayar da gas suna sayar da kilogram ɗaya tsakanin naira 1,600 zuwa 1,800.

A cewarsa, wadatar kayayyaki na ƙaruwa kuma farashin saye daga masu sarrafa gas yana tsakanin naira 1,300 zuwa 1,500 kan kilogiram, gwargwadon wurin da ake saye. Wannan ne ya sa su ma suke sayar wa masu amfani da farashin da ya dace da kuɗin sufuri da sauran kashe-kashe.

Tun da farko, an ruwaito cewa farashin gas na girki ya ƙaru da kusan kashi 140 cikin 100 a wasu yankunan ƙasar, lamarin da ya sa masu kasuwanci suka fara shirye-shiryen shigo da gas daga ƙasashen waje domin ƙara wadatar sa da rage tsada.

Daga matsakaicin naira 1,000 kan kilogram a watan Janairu da Fabrairu, farashin ya kai har naira 2,400 tsakanin watan Mayu da Yuni. Hakan ya sa hukumar da ke kula da harkar ta fara bayar da lasisin shigo da gas daga ƙasashen waje bayan da masana’antun cikin gida suka kasa biyan buƙatar da ake da ita.

A wani mataki na rage matsalar, Ministan Albarkatun Man Fetur Mai Kula da Harkokin Gas, Ekperikpe Ekpo, ya yi gargaɗi ga masu harkar da su guji ɓoye kayayyaki ko kuma cin moriyar jama’a ta hanyar ƙara farashi ba bisa ƙa’ida ba.

By ukarofi