Rangwamen farashin fetur ba dawo da tallafi ba ne – Idris

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ya yi ƙarin haske akan matakin Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), na rangwamen farashi na tsawon kwana 30, inda ya ce hakan ba ya nufin dawo da tallafin fetur, saida an yi haka ne don samar da sauƙin wucin-gadi ga halin matsi da al’umma suke ciki a sanadiyyar hauhawar farashin kayan makamashi a matakin ƙasa-da-ƙasa.

Mohammed Idris ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 12 ga Oktoba, 2026 yayin wata hira da manyan ‘yan jarida, inda ya bayyana tsarin gyare-gyaren tattali na Gwamnatin Tarayya da zayyano matakan da take ɗauka domin samar da sauƙi ga tsadar farashin kayayyaki.

Ministan ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana aiki tuƙuru wajen ganin ta samar da hanyoyin inganta halin zamantakewa, ɗorewar farfaɗowar tattalin arziƙi da tabbatar da cewa amfanin gyare-gyaren ya kai ga magidanta a faɗin Nijeriya.

Da yake bayani kan hikimar da ta sa aka samar da shirin ragin na NNPC, Idris ya ce kamfanin ya zaɓi ya yafe wani kaso na ribar da yake samu ne domin rage tasirin da farashin fetur ke yi akan sauran kayayyakin amfanin al’umma na yau da kullum. Ministan ya yarda cewa magidanta na fuskantar matsin tattali a ƙasar, inda ya ce wajibi ne shirin gyare-gyaren gwamnatin ya zama silar inganta rayukan talakawan Nijeriya.

Ya bayar da misali da sauƙin hauhawar farashi, ƙarfin rarar kuɗaɗen Nijeriya a asusun ƙasashen waje da ƙarin kuɗin shiga daga man da ba shigo da shi ake yi ba a matsayin alamun nasara a harkar tattali, yana mai amincewa da buƙatar a tabbatar da cewa al’umma suna amfana da ribar hakan.

Kazalika, ya tunatar da matsayar Shugaba Bola Tinubu ta cewa za a riƙa sake tsarin mafi ƙarancin albshin ma’aikata a kowane wa’adin bayan shekara uku a madadin shekara biyar da aka saba yi a baya.

By Babaji

Leave a Reply