
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun tsaro ƙarƙashin haɗakar JTF na Atisayen Haɗin Kai, sun yi nasarar halaka sama da mayaƙan ISWAP 40, ciki har da wani sanannen kwamanda, a wani hari ta sama da suka ƙaddamar a Jihar Borno.
An gudanar da atisayen ne a ranar 10 ga Oktoba, a yankin ƙauyen Badu da ke kudancin Gudumbali a Ƙaramar Hukumar Guzamala ta Jihar Borno, kamar yadda rundunar ta sanar.
Rundunar Sojoji ta ce farmakin ya biyo bayan samun wasu bayanai ne na sirri a game da wasu mayaƙan ISWAP daga yankin suna shirin ƙaddamar da hari akan dakarun soji da ke aiki a Sashe na 3 na Atisayen Haɗin Kai. Akan haka ne dakarun suka hanzarta kai musu hari a wani gida da mayaƙan suka mayar da shi mafaka gabanin aiwatar da shirin nasu.
Binciken sirrin dakarun ya nuna cewa an halaka sama da ‘yan ta’adda 40 a harin, ciki har da kwamandan, wanda aka sani da Ƙaid.
Rundunar Sojin ta bayyana atisayen a matsayin ɓangare na ƙoƙarin lalata hanyoyin gudanar da ayyukan ‘yan ta’adda da karya ƙarfin kai hare-harensu da kuma bayar da kariya ga hare-haren da suke shirya kai wa sansanonin sojoji da ƙauyukan fararen hula a Arewa maso Gabas.
Haka kuma, harin sojin ya yi sanadiyyar lalata babura guda 20 baya ga kisan mayaƙan, motoci biyu da ƙarin wasu babur 20 da ake zargin da su ne ‘yan ta’addar suke safarar kayayyakin amfaninsu na yau da kullum da kuma aiwatar da wasu munanan hare-hare a shiyyar.
