Hisbah ta kama ɗaliba cikin otel a Birnin Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Hukumar Hisbah ta jihar Kebbi ta sanar da kama wata ɗaliba da ba a bayyana sunan ta ba a wani Otel da ke anguwar Badariya cikin garin Birnin Kebbi Litinin ɗin nan.

Hukumar ta bayyana cewa sun sami labarin ganin ta da wannan yarinyar da hijab na wata Islamiyya ne ta shiga Otel ɗin inda suka isa wajen kuma suka yi nasarar kama ta tare da wani mutum kafin su aikata abinda ya kai su.

Yanzu haka dai ana cigaba da bincike kuma tare da ɗaukar matakan da suka kamata kan wannan yarinyar da kuma mutumin.

Hukumar ta yi kira ga iyaye da su riƙa saka ido kan ‘ya’yan su musamman mata da ya ke lalacewa ta fi muni a ɓangaren su, su ƙara kula da zirga-zirgar ‘ya’yansu, su tabbatar da cewa suna zuwa makaranta da gaske, tare da bibiyar halayensu da abokan hulɗarsu. Malamai da shugabannin makarantu su ƙarfafa tsarin sa ido kan halartar ɗalibai tare da sanar da iyaye idan ɗalibi ko ɗaliba ba ta halarci karatu ba.
Haka-zalika hukumar ta yaba wa mazauna anguwar bisa ga irin gudummawar da su ke bai wa hukumar wajen samun nasarar aiwatar da ayyukan ta.

By ukarofi

Leave a Reply