Ba za mu riƙa tona asirin masu aikata saɓo a ɓoye ba – Sabon kwamandan Hisbah a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sabon Kwamandan hukumar hisbah ta Jihar Katsina, Sheikh Saifuddin Yakubu Musa, ya bayyana cewa hukumar ba za ta riƙa bibiyar mutanen da ke aikata saɓo a ɓoye domin kama su da tona musu asiri ba.

Sheikh Saifuddin ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan wasu daga cikin sauye-sauye da gyare-gyaren da yake shirin aiwatarwa domin inganta ayyukan hukumar a jihar.

A cewarsa, hukumar za ta mayar da hankali wajen gudanar da ayyukanta bisa ƙa’idojin addinin Musulunci, musamman wajen kiyaye mutuncin al’umma da kauce wa tona asirin waɗanda ke aikata laifuffuka a ɓoye.

“Hukumar Hisbah ba za ta bi mutum da ya ɓoye kansa yana aikata saɓo ba, ta kama shi har ta tona masa asiri. Wannan yana daga cikin gyare-gyaren da za mu yi wa ayyukan Hisbah a jihar,” in ji Sheikh Saifuddin Yakubu Musa.

By ukarofi

Leave a Reply