Babu diyya ga kadarorin da ‘yan Nijeriya suka bari, inji gwamnatin Afirka ta Kudu

Spread the love

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta bayyana cewa, ba za ta biya ’yan Nijeriya diyya ba akan kadarorin da suka bari a ƙasar bayan an kwashe su zuwa Nijeriya.

Gwamnatin ta jaddada cewa duk wata kadara da aka mallaka ba bisa ka’ida ba, ko kuma wadda ke cikin matsugunan da ba su da izinin gwamnati (informal settlements), ba za ta cancanci a biya mata kowace irin diyya ba.

Wannan matsaya ta sake fitowa ne daga bakin Ministar da ke Fadar Shugaban Ƙasa ta Afirka ta Kudu, Khumbudzo Ntshavheni, wadda ta yi watsi da ra’ayin cewa gwamnatin Pretoria za ta biya ’yan Najeriya da suka rasa ko suka bar kadarorinsu yayin rikice-rikicen da suka gabata.

Kalaman nata sun biyo bayan bayyana da Mukaddashin Babban Kwamishinan Najeriya a Afirka ta Kudu, Temitope Ajayi, ya yi cewa gwamnatin Najeriya na duba yiwuwar hanyoyin da za a bi wajen neman diyya ga ’yan kasar da suka rasa ko suka bar kadarorinsu bayan an kwashe su daga Afirka ta Kudu.

Da take mayar da martani yayin ganawa da manema labarai, Ntshavheni ta ce babu wani dalili na doka da zai sa gwamnatin Afirka ta Kudu ta biya irin wannan diyya.

Ta bayyana cewa duk wata halastacciyar kadara a kasar tana da rijista a hukumomin da abin ya shafa, yayin da gine-ginen da ke cikin matsugunan da ba su da izini ba su da halacci a gaban doka.

Ministar ta shawarci bakin hauren da ke da kadarorin da suka mallaka bisa doka da su sayar da su ta hanyar kasuwar gidaje da kadarori ta Afirka ta Kudu, maimakon jiran gwamnati ta biya su diyya.

Ta ce, duk wanda yake da halastacciyar kadara ya sayar da ita a kasuwar kadarori,
Ta kuma jaddada cewa gwamnati ba za ta ɗauki alhakin kadarorin da aka bari ba.

Har ila yau, Ministar ta sake kira ga gwamnatin Najeriya da ta bai wa hukumomin Afirka ta Kudu bayanai kan wuraren da ake zargin ana gudanar da harkokin miyagun ƙwayoyi, tana mai cewa hakan zai taimaka wa jami’an tsaro wajen yaƙar ƙungiyoyin masu aikata manyan laifuka.

Wannan sabuwar musayar kalamai ta ƙara nuna irin ƙalubalen da ke tattare da dangantakar Najeriya da Afirka ta Kudu dangane da yadda ake mu’amala da ’yan Najeriya da ke zaune a can.

Dangantakar kasashen biyu ta shiga tsaka mai wuya bayan hare-haren ƙiyayya ga baƙin haure (xenophobia) da suka auku a baya-bayan nan.

A lokacin hare-haren, an yi wa shaguna da kadarorin baƙin haure, ciki har da na ’yan Najeriya, fashi, lalata da kuma ƙonewa a birane da dama na Afirka ta Kudu.

Sakamakon wannan tashin hankali, gwamnatin Najeriya ta kwashe daruruwan ’yan kasarta ta hanyar wani shirin dawo da su gida bisa taimakon gwamnati.

Hare-haren sun fuskanci Allah wadai daga ƙasashen Afirka, inda Najeriya ta bukaci a samar wa ’yan kasarta da jarinsu kariya mafi inganci a Afirka ta Kudu.

Daga bisani, gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi alƙawarin ƙarfafa tsaro tare da gurfanar da waɗanda suka aikata laifukan, yayin da kasashen biyu suka kafa hanyoyin diflomasiyya domin inganta dangantakarsu da kuma magance matsalolin da suka shafi ƙaura, aikata laifuka da kuma tsaron baƙin haure.

By Babaji

Leave a Reply