Aƙalla mutum biyar ne suka rasa rayukansu bayan wata mummunar gobara ta tashi a wani katafaren ginin bene mai hawa goma da ke birnin Antwerp na ƙasar Belgium a safiyar Laraba, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici wanda cikin ƙanƙanin lokaci aka fara gagarumin aikin ceto.
‘Yan sandan Belgium sun tabbatar da faruwar lamarin, sai dai sun bayyana cewa har yanzu ba a iya tantance adadin mutanen da suka jikkata ko kuma gano musabbabin tashin gobarar ba.
Tun da farko wasu kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun rawaito cewa mutum shida ne suka mutu, bisa bayanan farko daga ‘yan sanda. Sai dai daga baya hukumomi sun sake duba bayanan tare da tabbatar da cewa adadin waɗanda suka mutu ya kai biyar.
Wakilan Reuters da ke wurin sun shaida yadda jami’an ceto suka yi amfani da igiyoyi wajen saukar da wasu mazauna daga gefen ginin, yayin da wasu kuma aka kuɓutar da su ta amfani da babbar matakalar motocin kashe gobara.
Waɗanda suka tsira sun bayyana cewa suna zaune cikin gidajensu bayan gobarar ta bazu cikin sauri, kafin jami’an ‘yan sanda da masu kashe gobara su isa wurin jim kaɗan bayan tashin gobarar.
