Sakkwato: ‘Yan bindiga sun halaka hakimi, ɗansa da wasu biyar yayin da matasa suka tare babban titi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu ‘yan bindiga sun halaka Hakimin yankin Kulodo da ke Ƙaramar Hukumar Bodinga a Jihar Sakkwato, Alhaji Abubakar Tudu, tare da babban ɗansa da wasu mutum huɗu a wani sabon hari da suka ƙaddamar a ƙauyukan Kulodo da Kwance.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kutsa cikin ƙauyukan ne tare da kai farmaki kan mazauna yankin, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka da tayar da fargaba acikin jama’ar yankin.

Haka kuma, hari ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda wanda mazaunin ƙauyen Kwance ne, lamarin da ya matasa da dama suak yi cincirindo suak tare hanyar Sakkwato zuwa Jega, idna suek nuna adawarsu ga yawan hare-hare a Ƙaramar Hukumar Bodinga.

Harin ya haddasa jimamin al’ummar yankin, yayin da mazauna ke kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa domin kamo waɗanda suka aikata laifin tare da ƙarfafa tsaro a yankunan da abin ya shafa.

A cewar mazauna yankin, kimanin ‘yan bindiga 150 akan babura ne aka suka kai farmakin, waɗanda aƙalla akwai mutum biyu zuwa uku a kowane babur.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan harin ba, yayin da ake cigaba da tattara bayanai kan al’amarin.

By Babaji

Leave a Reply