Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Fansan Yamma sun ceto hakimin Farin Hawa da ke ƙaramar hukumar Malumfashi a Jihar Katsina, bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 2 lokacin da maharan suka kai hari ƙauyen Farin Hawa inda suka sace hakimin, Alhaji Mubarak Sharin.
Rundunar ta ce bayan samun bayanan sirri, dakarunta tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun bi sahun maharan, inda suka yi musayar wuta da su.
A cewar sanarwar, an kashe ɗaya daga cikin maharan, yayin da sauran suka tsere, lamarin da ya bai wa dakarun damar kuɓutar da hakimin ba tare da ya samu rauni ba.
Har ila yau, rundunar ta ce a wani samame da aka kai tsakanin Amara da Chakau a ƙaramar hukumar Ɗanmusa, dakarun sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, jigidar harsashi ɗaya mai ɗauke da harsasai takwas da kuma babura guda biyu da ake zargin maharan na amfani da su.
Haka kuma, a wani artabu da aka yi a yankunan Sabon Gari da Dantakeri na ƙaramar hukumar Dutsinma, rundunar ta ce an kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne, yayin da wasu suka tsere.
Operation Fansan Yamma ta ce waɗannan hare-hare na daga cikin ci gaba da matakan da take ɗauka domin daƙile ayyukan ‘yan bindiga da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin Arewa maso Yamma.
Sojoji sun ceto hakimin Farin Hawa daga hunnun ‘yan bindiga a Katsina
