Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Yayin da saura kusan watanni shida kacal a gudanar da babban zaɓen shekarar 2027, manyan jam’iyyun adawa a Nijeriya na ci gaba da fuskantar rikice-rikicen shugabanci da ƙararrakin kotu, lamarin da ke ƙara raunana su a daidai lokacin da jam’iyyar APC mai mulki ke ƙarfafa tsarinta domin tunkarar zaɓen.
Daga Jam’iyyar PDP, zuwa ADC, LP da kuma NDC, kusan dukkaninsu na fama da rarrabuwar kawuna, shugabanni masu taƙaddama, tarukan zaɓen fidda gwani daban-daban da kuma jerin shari’o’in kotu da suka dabaibaye harkokinsu.
Lamarin ya jefa dubban ’yan takarar da aka tantance domin shiga zaɓen 2027 cikin damuwa, yayin da da dama ke fargabar ko jam’iyyun da suke son tsayawa takara a ƙarƙashinsu za su tsallake waɗannan matsalolin shari’a kafin lokacin zaɓe.
A cikin Jam’iyyar PDP, rikicin ya kai ga gudanar da zaɓen fidda gwani sau biyu, wanda ya haifar da fitowar ’yan takarar shugaban ƙasa biyu daban-daban.
Kwamitin Gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Abdulraman Mohammed, wanda ke samun goyon bayan Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya tsayar da tsohon Sanatan jihar Kuros Riba, Sandy Onor, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP.
Sai dai a ɗaya ɓangaren kuma, Kwamitin Riƙon ƙwarya na jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ya ce tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, shi ne halastaccen ɗan takarar PDP.
Makon da ya gabata, ɓangarorin biyu sun gudanar da bukukuwan rabon takardun shaidar nasara ga ’yan takararsu daban-daban, abin da ya ƙara nuna zurfin rikicin da ke addabar jam’iyyar.
A halin yanzu dai ɓangaren Abdulraman Mohammed ne ke da rinjaye, kasancewar shi ne Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta amince da shi. Sai dai ɓangaren Tanimu Turaki ya kai ƙara kotu domin neman umarnin da zai tilasta wa INEC amincewa da shi a matsayin halastaccen shugabancin PDP.
Yayin da yake jawabi a wani taron Kwamitin Zartarwa na ƙasa (NEC) na PDP a Abuja, Wike ya bayyana cewa an riga an gama yaƙin neman iko a jam’iyyar, yana mai cewa mafi munin lokacin rikicin ya wuce. Sai dai kakakin ɓangaren Turaki, Ini Ememobong, ya yi watsi da wannan ikirari, yana mai cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne sunayen ’yan takarar da za su bayyana a takardar zaɓe.
A jam’iyyar ADC, wadda ta yi ƙoƙarin zama dandalin haɗakar jam’iyyun adawa domin tunkarar zaɓen 2027, rikicin ma bai yi ƙasa a gwiwa ba. Jam’iyyar ta kasu gida uku: akwai ɓangaren da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Daɓid Mark, ke jagoranta, wanda INEC ke amincewa da shi; akwai kuma ɓangaren Kingsley Ogga, da kuma na tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na ƙasa, Nafiu Bala.
ɗaya daga cikin fitattun magoya bayan ɓangaren David Mark shi ne tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar. Sakataren Yaɗa Labarai na ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya tabbatar da cewa jam’iyyar na fuskantar ƙarar shari’a uku daban-daban, ciki har da wadda Nafiu Bala ya shigar kan shugabancin David Mark. A cewarsa, duk da waɗannan matsaloli, ADC ba za ta bari shari’o’in su hana ta shirye-shiryen zaɓe ba.
A ɓangaren Jam’iyyar LP, rikicin ya kai matakin da ya samar da shugabanci biyu, tarukan jam’iyya daban-daban da kuma ’yan takarar shugaban ƙasa biyu.
ɓangaren da Nenadi Usman ke jagoranta ya tsayar da Dr. Chibuzo Okereke a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa. Sai kuma ɓangaren tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Julius Abure, wanda ya zaɓi Prince Kennedy Ahanotu a matsayin ɗan takararsa. Mataimakin Shugaban LP na ƙasa a ɓangaren Abure, Dr. Ayo Olorunfemi, ya ce Kotun ƙoli ce kaɗai za ta iya kawo ƙarshen taƙaddamar shugabancin jam’iyyar. Sai dai wasu jiga-jigan LP suna ganin an riga an warware rikicin, suna mai cewa ƙoƙarin ɓangaren Abure ba zai canja komai ba.
A gefe guda kuma, sabuwar matsala ta kunno kai a Jam’iyyar NDC, wadda a baya-bayan nan ta fara jan hankalin wasu fitattun ’yan siyasar adawa. Rikicin ya samo asali ne bayan wata kotun tarayya ta soke hukuncin da ta yanke a baya wanda ya tilasta wa INEC rajistar jam’iyyar. Sai dai shugabannin NDC sun dage cewa hukuncin bai soke rajistar jam’iyyar ba, kuma sun ce sun ɗaukaka ƙara zuwa Kotun ɗaukaka ƙara.
Shugaban NDC na ƙasa, Cleopas Zuwoghe, ya bayyana cewa har yanzu jam’iyyar na da cikakken yaƙinin samun nasara a kotu, yana mai cewa kotun tarayya ba ita ce matakin ƙarshe na shari’a a ƙasar ba.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa irin waɗannan rikice-rikice da suka dabaibaye PDP, ADC, LP da NDC na iya rage ƙarfin jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.
Jiga-jigan adawa dai suna zargin cewa yawaitar shari’o’in da suka addabe su wani shiri ne da gwamnatin APC ke amfani da shi wajen raunana abokan hamayyarta kafin zaɓe.
Sai dai jam’iyyar APC da na kusa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun sha musanta wannan zargi, suna mai cewa ba su da hannu a rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyun adawa.
