Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mazauna ƙauyen Kurawa da wasu ƙauyukan da ke maƙwabtaka da shi a ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato sun zargi wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne da dasa wani bom a kan hanyar Sabon Birni zuwa Kurawa bayan kai hare-hare a wasu ƙauyukan yankin.
Rahoton ya bayyana cewa mazauna yankin sun ce an dasa bom ɗin ne da sanyin safiyar Lahadi domin hana jami’an tsaro da ke Sabon Birni samun damar kai ɗauki cikin gaggawa bayan samun kiran neman agaji daga al’ummomin da aka kai wa hari.
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya ce dimbin ‘yan bindiga ɗauke da makamai, waɗanda suka zo a kan babura, sun afka wa ƙauyen Kurawa da misalin ƙarfe ɗaya na dare a ranar Lahadi.
A cewarsa, maharan sun kashe wani mazaunin ƙauyen mai suna Sabiu Yakubu, sun raunata wasu mutane tare da kwashe dukiyoyi da suka haɗa da dabbobin gida.
“Duk lokacin da muka kira sojoji idan an kai mana hari suna ƙoƙarin kai ɗauki. Amma a wannan karon, bayan mun sanar da su, ba su samu damar zuwa ba sai bayan maharan sun bar yankin,” inji shaidar.
Ya danganta jinkirin da aka samu wajen kai ɗaukin jami’an tsaro da harin bom da aka kai a Bargaja kwanan nan, wanda rahotanni suka ce ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro uku.
Shaidar ta kuma bayyana cewa yayin da mazauna yankin ke cikin jimamin harin da safe, wani matashi mai suna Mudassir Salihu ya hau babur ɗin haya daga Kurawa zuwa Sabon Birni.
“Da suka yi kusan kilomita ɗaya daga Kurawa, babur ɗin ya taka bom ɗin. Direban da fasinjan sun samu munanan raunuka amma sun tsira da rayukansu,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, wata mota ƙirar Volkswagen Golf da ke bi ta wannan hanya ita ma ta taka wani bom da ake zargin an dasa, lamarin da ya lalata gaban motar tare da jikkata wasu daga cikin fasinjojinta. Lokacin da na isa wurin, babu wanda ya rasa ransa sakamakon fashewar bom ɗin, amma motocin sun lalace matuƙa,” ya ƙara da cewa.
Wani mazaunin Garin Zago, wanda surukinsa ya rasu a harin, ya ce tun kafin aukuwar lamarin al’umma sun samu bayanan sirri cewa kusan babura 20 ɗauke da ‘yan bindiga na tunkarar ƙauyukansu.
A cewarsa, mazauna yankin sun yi sintiri da dare kafin maharan su kai farmaki. “Mun kasance cikin sintiri lokacin da aka fara ruwan sama da misalin ƙarfe 1:40 na dare. Ba da jimawa ba suka fara harbe-harbe. Sun kashe Salisu Yakuba, sun harbi wani ɗan ƙungiyar sa-kai mai suna Basiru Dan Banga, sannan suka sace mutum uku. Sai dai biyu daga cikin wazanda aka sace sun tsere daga baya, inda Sani Yakuba kaɗai ya rage a hannunsu,” inji shi. Ya ce, maharan sun kuma tafi da shanu biyu.
Mazaunin ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su kawo ƙarshen hare-haren da ake ci gaba da kai wa yankin, yana mai zargin cewa galibi ana yi wa mazauna barazana idan suka fito fili suna magana kan matsalar tsaro.
“Idan muka bayyana abin da ke faruwa da mu, sai a ce muna adawa da gwamnatin jihar. Duk da haka, hare-haren na ci gaba ba tare da samun isasshen ɗauki ba,” ya koka.
Wani masani kan harkokin tsaro da ke zaune a Sokoto ya kuma yi iƙirarin a wani rubutu da ya wallafa a Facebook cewa an hangi sama da mutum 10 dauke da makamai, waɗanda ake zargin mabiyan fitaccen jagoran ‘yan bindiga Bello Turji ne, suna ƙoƙarin dasa bom a kusa da Kurawa a daren Asabar kafin kai harin.
A cewarsa, mutanen suna sanye da na’urorin hangen dare yayin gudanar da aikin. Ya kuma yi zargin cewa bom ɗin da suka dasa ne ya lalata mota da babur bayan harin. Sai dai ba a samu wata hujja mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan iƙirari ba.
ƙoƙarin jin ta bakin Kakakin Rundunar :Yan Sandan Jihar Sakkwato, Mataimakin Sufetan ‘Yan Sanda Ahmad Rufai, da kuma ɗan Majalisar Dokokin Jihar Sokoto mai wakiltar mazaɓar Sabon Birni ta Arewa, Aminu Boza, bai yi nasara ba, domin ba su amsa kira ko saƙonnin da aka aika musu ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.
Wannan sabon hari ya zo ne kwanaki takwas kacal bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun tayar da bom da aka dasa domin kai hari ga jami’an tsaro a kusa da Bargaja, a ƙaramar Hukumar Isa. Rahotanni sun ce harin ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro uku, tare da nuna yadda ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke ƙara amfani da bama-bamai a yankin Gabashin Sakkwato.
Mazauna yankin sun bayyana cewa karuwar amfani da irin waɗannan bama-bamai ya ƙara jefa al’ummomin Sabon Birni, Isa, Goronyo da sauran sassan Gabashin Sakkwato cikin fargaba, domin yanzu barazanar ba ta tsaya ga jami’an tsaro kaɗai ba, har da matafiya, manoma da mutanen da suka rasa matsugunansu da ke ƙoƙarin komawa garuruwansu.
