Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sabbin bayanai sun bayyana kan yadda aka kashe Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na Jihar Benuwai, Alhaji Ardo Risku Muhammad, inda iyalansa suka yi zargin cewa an yi masa kwanton ɓauna ne bayan ya halarci wani taron sulhu da ‘yan sanda suka shirya tsakanin makiyaya da manoma.
Marigayin ya rasa ransa tare da abokinsa Yakubu Isah a ranar Juma’a yayin da suke komawa gida daga taron da aka gudanar a ƙaramar hukumar Ohimini.
ɗan marigayin, Muhammad Idris, ya ce mahaifinsa ya sanar da iyalansa da safe cewa zai halarci taron ne bisa gayyatar DPO na Ohimini. Ya ce saboda lalacewar hanya, mahaifinsa ya bar motarsa, ya hau babur tare da Yakubu Isah.
A cewarsa, bayan sun isa ofishin ‘yan sanda, sai mahaifinsa ya tarar cewa shugabannin ƙaramar hukuma da sarkin yankin da aka ce za su halarta ba su zo ba. An tattauna batutuwan da suka shafi rikicin makiyaya da manoma kafin a kammala taron.
Idris ya ce bayan sun bar wurin taron ne aka yi musu kwanton ɓauna tare da harbe mahaifinsa da Yakubu Isah har lahira, kimanin kilomita biyu zuwa uku daga Ohimini.
Iyalan mamacin sun buƙaci gwamnatin jihar Benue da Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya da sauran hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka kashe marigayin da kuma tabbatar da an yi adalci.
A nasu ɓangaren, shugabannin ƙananan hukumomin yankin Idoma tare da Mai Bai Wa Gwamna Shawara kan Harkokin Tsaro sun yi Allah-wadai da kisan, suna mai cewa aikin wasu masu laifi ne da ke son tayar da zaune tsaye.
Shugaban ƙaramar hukumar Ohimini, Gabriel Adole, ya ce marigayin mutum ne mai son zaman lafiya kuma yana da kyakkyawar alaƙa da al’ummomin yankin. Ya roƙi Fulani su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’an tsaro damar gudanar da bincike.
Shi ma shugaban ƙaramar hukumar Agatu, James Melɓin Ejeh, ya ce bai kamata a ɗora laifin kisan kan al’ummar Idoma ba, yana mai jaddada cewa wasu bata-gari ne suka aikata hakan domin kawo cikas ga zaman lafiyar da aka fara samu a jihar.
Mai Bai Wa Gwamnan Benue Shawara kan Tsaro, Chief Joseph Har, ya bayyana kisan a matsayin abin takaici, yana mai cewa marigayin sanannen mai fafutukar zaman lafiya ne. Ya kuma yi kira ga iyalansa da magoya bayansa da su guji ɗaukar doka a hannunsu.
A halin da ake ciki, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Benue ta sanar da kama mutane 10 da ake zargi da hannu a kisan.
Kakakin rundunar, DSP Udeme Edet, ta ce bincike ya yi nisa, yayin da Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Cletus Nwadiogbu, ya tabbatar da cewa za a ci gaba da bincike har sai an kamo duk masu hannu a lamarin.
Shugabancin ƙasa na MACBAN ya yi Allah-wadai da kisan, tare da bayyana marigayin a matsayin jagoran zaman lafiya wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen sasanta rikice-rikicen makiyaya da manoma a Benue.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Baba Othman Ngelzarma, ya ce ƙungiyar ba za ta bari a rufe shari’ar ba tare da hukunta masu laifi ba. Sai dai ya roƙi mambobinta su kwantar da hankalinsu su guji ɗaukar fansa.
Hakazalika, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, sun yi tir da kisan, tare da kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci domin gurfanar da masu hannu a gaban kotu.
A wani ci gaba kuma, dakarun Operation Whirl Stroke (OPWS) sun kashe wasu da ake zargin ‘yan ta’adda biyu bayan sun daƙile wani hari da aka shirya kai wa kasuwar doya ta Tor Donga da ke ƙaramar hukumar Katsina-Ala a jihar Benue.
Jami’an sun ce sun ƙwato bindigar AK-47, bindigar hannu, alburusai da wasu kayayyaki daga hannun waɗanda aka kashe, yayin da suka yaba da haɗin kan al’umma wajen bai wa jami’an tsaro bayanan sirri da suka taimaka wajen nasarar aikin.
