Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Kamfanin Optimal Image Media Limited da gidan tababijin na 3rd Eye Africa TV, Alhaji Shu’aibu Mungadi, ya yaba wa Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamred (Dr.) Nasir Idris, bisa irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu wajen inganta tsaro da kuma aiwatar da ayyukan ci gaba a faɗin jihar tasa.
Alhaji Mungadi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin da tawagar yaɗa labarai ta Gwamnatin Jihar Kebbi, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Yakubu Ahmed BK, ta kai masa ziyarar haɗin gwiwa a ofishinsa da ke Abuja.
Ya ce, yadda gwamnatin Nasir Idris ta tunkari matsalar rashin tsaro ya cancanci yabo, yana mai ƙara da cewa gwamnati ta samar wa jami’an tsaro kayan aiki da tallafin da suka taimaka wajen rage ayyukan masu aikata laifuka a jihar.
A cewarsa, a matsayinsa na ɗan asalin Jihar Kebbi, ya san irin halin da jihar ke ciki kafin wannan gwamnati ta hau mulki, amma yanzu an samu sauyi mai ma’ana da ya inganta martabar jihar tare da sauya fasalin babban birnin jihar.
Mungadi ya danganta nasarorin da gwamnatin ta samu da jajircewar Gwamna Nasir Idris wajen gudanar da mulki nagari da kuma kusancinsa da al’umma, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai sauraron jama’a kuma mai ba su fifiko.
Ya kuma tabbatar wa tawagar yaɗa labaran gwamnatin jihar cewa kamfanonin Optimal Image Media Ltd da 3rd Eye Africa TV za su ci gaba da ba ayyukan gwamnatin Kebbi cikakken goyon bayan yaɗa labarai, tare da ƙalubalantar duk wani yaɗa bayanan ƙarya ko yunƙurin ɓata sunan gwamnatin.
A nasa jawabin, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Ahmed BK, ya gode wa 3rd Eye Africa TV bisa yadda tashar ke ci gaba da haska ayyukan gwamnatin Gwamna Nasir Idris.
Ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da kafar yaɗa labaran domin ci gaba da isar da sahihan bayanai game da ayyukan gwamnati ga jama’a.
Kwamishinan ya ce gwamnatin Nasir Idris ta samu gagarumar nasara a fannoni da dama, ciki har da gina da gyaran hanyoyi, sabunta makarantu, asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko, tare da aiwatar da sauran ayyukan raya ƙasa a ƙananan hukumomi 21 na jihar.
