Duk ma’aikacin Katsina da ba shi da takarda za mu kore shi, in ya so ya je ya zaɓi Firauna – Dikko Raɗɗa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya ce gwamnatin sa ba ta ɗaukar jahili aiki a jihar.

Gwamnan ya yi wannan magana ne a wajan bikin miƙawa malaman makarantun firamare da sakandire takardun kama aiki a Katsina.

Ya mai da martani ne kan wasu ma’aikatan gwamnatin jihar da aka dakatar suka kai ziyara ga wani ɗan takarar gwamnan Jihar ƙarƙashin ɗaya daga cikin jam’iyar adawa.

Ya ce gwamnati ta kafa kwamitin tantance ma’aikatan jihar Kuma sun gudanar da aikin su bisa ƙwarewa da adalci.

“Saboda haka idan an dakatar da ma’aikaci daga aiki to sai bashi da takardar karatu ko Kuma takardun na bogi,”inji Dikko.

Gwamnan sai ya tabbatar wa duk ma’aikacin da aka dakatar kuma alhanin yana da takardun sa to ya zo ya gabatar a sake tantance idan ba matsala a mai da shi aiki tare da biyan sa albashin sa na tsawon watannin da aka tsaida maka.

Ya nuna takaicin sa yadda ake so a siyasantar da matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka na tsarkake aikin a jihar.

“Duk ma’aikacin gwamnatin jihar Katsina da bashi da takardar karatu za mu kore shi in yaso ya je ya zaɓi Firauna” Raɗɗa ya ce.

By ukarofi

Leave a Reply