Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Uwargidan Shugaban ƙasa, Sanata Remi Tinubu, ta kare kalaman da ta yi kwanan nan game da tallafa wa ƙananan masu sana’o’i kamar ƙosai da gasasshen masara, tana mai cewa shirin tallafin Gwamnatin Tarayya bai tsaya ga masu sayar da ƙosai kaɗai ba, illa ya haɗa da nau’o’in ƙananan ’yan kasuwa daban-daban domin inganta rayuwarsu a ƙarƙashin manufar Sabunta Fata, wato Renewed Hope.
Remi Tinubu ta bayyana hakan ne ranar Litinin yayin ƙaddamar da ɗakin Taro na Abubakar Maje Haruna da ke Fadar Sarkin Hadejia a Jihar Jigawa, kwanaki kaɗan bayan da kalamanta kan masu sana’ar ƙosai, gasasshen masara da ƙuli-ƙuli suka haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta, musamman saboda halin ƙuncin tattalin arzikin da ake ciki a ƙasar.
Yayin da take jawabi a wajen taron, Uwargidan Shugaban ƙasar ta bayyana cewa shirin tallafin da ofishinta ke jagoranta bai taƙaita ga masu sayar da ƙosai ba. Ta ce ya kuma haɗa da masu sana’ar sayar da tumatur, barkono, kayan lambu da kuma gasasshen ayaba da aka fi sani da bole.
A yayin da take mayar da martani kan sukar da aka yi mata, Remi Tinubu ta sake jaddada goyon bayanta ga ƙananan ‘yan kasuwa, tana mai cewa manufar shirin ita ce ƙarfafa sana’o’in da dubban ‘yan Nijeriya ke dogaro da su wajen samun nufin askri.
Ta ce, “Na san ana ta cewa na ambaci ƙosai. Amma ba ƙosai kaɗai ba ne. Akwai masu sayar da tumatur, akwai masu bole, akwai masu barkono da masu kayan lambu a kasuwa. Za mu ci gaba da ƙarfafa su tare da ƙara musu jari domin sana’arsu ta ɗore.”
Uwargidan Shugaban ƙasar ta kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta bai wa Gwamnatin Jihar Jigawa tallafin Naira miliyan 100 domin tallafa wa ƙananan ’yan kasuwa 2,000 a jihar.
A cewarta, kowane wanda ya ci gajiyar shirin zai karɓi Naira 50,000 domin ƙara wa sana’arsa jari da tabbatar da ɗorewarta. Ta kuma jaddada cewa gwamnati ba za ta ja da baya ba saboda suka ko rahotannin da ta ce ba su dace ba da ake yaɗawa kan shirin.
“Na san wazanda suka amfana da wannan shiri suna yaba masa. Ba za mu bari rahotannin da ba daidai ba su razana mu ba. Za mu ci gaba da tabbatar da cewa jama’armu ta samu kulawar da ta dace.”
Remi Tinubu ta kuma ƙarfafa gwiwar matasan Nijeriya da su rungumi harkar noma, tana mai cewa ƙasar na da ɗimbin albarkatun noma da ba a yi amfani da su yadda ya kamata ba fiye da dogaro da man fetur kaɗai.
Ta kawo misalin wata gonar lemu da ta kai ziyara a Jihar Benuwe, tana mai cewa hakan ya nuna irin manyan damar da ke ɓoye a fannin noma, tare da kira ga matasa da su shiga wannan fanni domin bunƙasa tattalin arzikinsu da kuma ci gaban ƙasa.
