
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙasar Amurka ta janye da dama daga cikin dakarun tsaronta da ta tura wa Nijeriya domin aikin haɗaka da dakarun tsaro na daƙile ayyukan ta’addanci a yankin Tafkin Chadi, yayin da take cigaba da aiki tare da ƙasar akan lamuran leƙen asiri da wasu harkokin tsaro da hukumomin Nijeriya.
Kwamandan sojojin saman Amurka a Afirka, Janar Dagvin R.M. Anderson ne ya sanar da haka a wata tattaunawa da manema labarai akan sakamakon babban taron jagororin tsaron ƙasashen Afirka na 2026.
Ya ce, haɗakar ta tsakanin Washington da Abuja za ta cigaba da gudana musamman akan atisayen leƙen asiri da ke harin Islamic State (ISIS/Daesh).
A cewarsa, an samu yin nasarar cimma manufar da ta sa aka tura dakarun Amurkan zuwa Nijeriya, lamarin da ya sa aka ɗauki matakin janye su, yana mai cewa Amurka za ta cigaba da tallafa wa gwamnatin Nijeriya a lamuran tsaro musamman akan bayanan leƙen asiri.
A watan Fabrairu, 2026 ne dai Amurka ta tura wa Nijeriya kimanin sojoji guda 200 domin tallafa wa dakarun tsaron Nijeriya akan atisayensu na yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci a yankin Tafkin Chadi.
Gwamnatin Amurka ta ɗauki matakin ne bayan Shugaba Donald Trump ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa na musamman akanta.
