Kotu ta ba da belin Sowore kan miliyan N200

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa fitaccen mai fafutukar kare haƙƙin al’umma kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, belin Naira miliyan 200 a shari’ar da ake da shi inda ake zargin sa da aikata laifin da ya shafi intanet.

Hukumar ‘yan sandan farin kaya (SSS) ce ta gurfanar da editan jaridar Sahara Reporters bisa zargin cewa ya aikata laifin da ya saɓa da dokokin amfani da intanet bayan kiran shugaba Tinubu da “mai laifi” a wasu rubuce-rubucensa da ya wallafa a shafukan sada zumunta a bara.

Mai shari’a Mohammed Umar ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, inda kotun ta amince da bayar da belin tare da sharaɗin gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa.

Kotun ta yi umarnin cewa ɗaya daga cikin waɗanda za su tsaya masa dole ne ya kasance basarake daga garinsu yayin da na biyun kuma dole ne ya mallaki kadara a Abuja.

Haka kuma, kotun ta umarci masu gabatar da ƙara su tantance sahihancin waɗanda za su tsaya masa.

A matsayin wani ɓangare na sharuɗɗan belin, kotun ta umurci Sowore ya miƙa fasfo ɗinsa na ga mataimakin babban magatakardar kotun.

Daga nan ne Mai shari’a Umar ya sallami Sowore sannan ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar Litinin, 6 ga watan Yuli domin ya fara kare kansa.

ƙungiyar Take It Back ta yi Allah-wadai da sharuɗɗan belin.

Jim kaɗan bayan yanke hukuncin, ƙungiyar Take It Back Moɓement ta soki sharuɗɗan belin da kotun ta gindaya wa Sowore, tana mai bayyana su a matsayin masu tsauri, danniya da kuma wuce gona da iri.

A cikin wata sanarwa da Ko’odinetan ƙungiyar na ƙasa, Juwon Sanyaolu, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce sharuɗɗan sun yi kama da hukunta wanda ba a same shi da laifi ba tare da yunƙurin takurawa da tsoratar da Sowore.

ƙungiyar ta yi suka musamman kan buƙatar gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa ciki har da wani basarake daga garinsu da kuma mai kadara a Abuja, kowannensu da darajar Naira miliyan 200 da kuma miƙa fasfo ɗinsa.

A cewarta, waɗannan sharuɗɗan ba su da alaƙa ta kai tsaye da tabbatar da halartar Sowore kotu, kuma suna ƙara ƙarfafa zargin cewa shari’ar na da alaƙa da siyasa fiye da neman adalci.

ƙungiyar ta kuma yi tuni kan cewa Sowore ya kasance yana halartar kotu a duk lokacin da aka buƙace shi. Saboda haka, ta ce soke belinsa, tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje da kuma sabbin sharuɗɗan belin sun ƙara haifar da damuwa cewa ana amfani da hukumomin gwamnati wajen murƙushe masu bayyana ra’ayinsu.

ƙungiyar ta buƙaci kotun ta sake duba sharuɗɗan belin bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Nijeriya da suka shafi adalci, daidaito.

A makon da ya gabata ne Babbar Kotun Tarayya ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar da Sowore ya gabatar na mayar masa da belinsa bayan ta saurari hujjojin ɓangarorin biyu.

Lauyansa, R.O. Adakole, wanda ya wakilci, Adeyinka Oyesile-Fusika (SAN), ya roƙi kotun ta dawo masa da belin da aka ba shi tun farko, yana mai cewa hakan ne ya dace da batun yi masa adalci. Haka kuma ya buƙaci kotun ta yi watsi da martanin masu gabatar da ƙara.

Sai dai lauyan masu gabatar da ƙara, Akinlolu Kehinde (SAN), ya nuna rashin amincewa da buƙatar, yana mai cewa Sowore bai gabatar wa da kotu cikakkun hujjoji masu inganci da za su sa ta yi amfani da ikonta wajen amincewa da buƙatarsa ba.

Buƙatar dai ta biyo bayan hukuncin da kotun ta yanke a ranar 16 ga Yuni na soke belin da ta bai wa Sowore tare da bayar da sammacin kama shi bayan da ya gaza halartar zaman kotu.

An kama shi bayan zaman kotun na ranar 23 ga watan Yuni, sannan aka tsare shi a gidan yarin Kuje har sai da aka yanke hukunci kan buƙatarsa ta dawo masa da beli.

Maimakon ya fara kare kansa, Sowore ya buƙaci mai shari’a Umar ya janye daga sauraron shari’ar, yana mai zarginsa da nuna son kai.

Sai dai alkalin ya ƙi amincewa da buƙatarsa, yana mai cewa ba a gabatar da hujjoji masu gamsarwa da za su sa ya janye ba, tare da umarnin ci gaba da sauraron shari’ar.

Hukumar SSS ta gurfanar da Sowore a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja ne a watan Disambar 2025 kan zargin aikata laifi da suka shafi intanet sakamakon rubuce-rubucen da ya wallafa a shafukansa X da Facebook, inda ya kira Shugaba Tinubu “mai laifi.”

Sai dai Sowore ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa, kuma tun farko kotun ta ba shi beli bisa amincewa da kansa.

By ukarofi