Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shekaru biyu bayan Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimi domin ceto ɓangaren daga shekaru na sakaci, cunkoson azuzuwa da kuma yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta, sabon rahoton ƙidayar Makarantu Ta Shekara ya nuna cewa har yanzu makarantun firamare na gwamnati a jihar na fama da matsanancin ƙarancin malamai, inda malami guda ke koyar da ɗalibai har 105.
Rahoton ƙidayar Makarantu Ta Shekara na 2024/2025, wanda shi ne sabon cikakken nazarin da gwamnatin jihar ta gudanar kan harkokin ilimi, ya nuna cewa rabon ɗalibai da malamai a makarantun gwamnati na matakin firamare da na ƙananan yara ya kai 105 zuwa malami ɗaya. Wannan adadi ya zarce aa’idojin ƙasa da na duniya duk da ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimi, ware kuɗaɗe masu yawa da kuma ɗaukar dubban malamai aiki.
Bisa ga rahoton, a makarantun sakandiren ƙasa rabon ɗalibai da malamai ya kai 50 zuwa ɗaya, yayin da a makarantun sakandiren gaba da sakandire ya kai ɗalibai 37 ga malami ɗaya.
Wannan ya yi nisa da ƙa’idojin da ake so a bi. Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar ɗinkin Duniya (UNESCO) ta tanadi cewa ya kamata malami ɗaya ya kula da ɗalibai 25 kacal a matakin firamare.
Haka kuma, Manufofin Ilimi na ƙasa sun tanadi rabon malami ɗaya ga yara 25 a matakin ƙananan yara, 35 a firamare da kuma 40 a sakandire.
Sai dai rahoton ya nuna cewa makarantun firamare da dama, musamman a birane masu yawan jama’a, har yanzu suna aiki fiye da ƙa’idar da aka amince da ita saboda cunkoson ɗalibai da ƙarancin malamai.
Ko da yake an fitar da rahoton ne a watan Disamban 2025, Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa har yanzu shi ne sabon rahoton hukuma da ke nuna halin da fannin ilimi ke ciki a jihar.
Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da yawan masu karatu a makarantun gwamnati ya haura miliyan 5.6. Jimillar ɗalibai da yara masu karatu da aka yi wa rajista a lokacin binciken sun kai 5,690,634.
Daga cikin wannan adadi, yara 683,773 suna matakin ƙananan yara, ɗalibai 4,034,744 suna firamare, 509,314 suna sakandiren ƙasa, 412,518 suna sakandiren gaba da sakandire, 31,236 suna makarantun kimiyya da fasaha, yayin da 19,049 ke cibiyoyin ilimin manya da na waɗanda ba su samu damar yin karatun boko ba.
Rahoton ya bayyana cewa wannan yawan ɗalibai ya jefa makarantu cikin matsin lamba mai tsanani ta fuskar malamai, azuzuwa da sauran kayayyakin more ilimi, lamarin da ke haifar da damuwa kan ingancin koyarwa da koyo.
Wani babban ƙalubalen kuma shine cunkoson azuzuwa. Binciken ya nuna cewa a matsakaici yara 145 ne ke amfani da aji guda a makarantun firamare da na ƙananan yara, yayin da a sakandiren ƙasa aji guda ke ɗaukar ɗalibai 78, sannan a sakandiren gaba da sakandire ya kai 69.
ɓangaren banɗakuna ma ya nuna matsalar cunkoso. A matsakaici, bayan gida guda yana amfani da yara 343 a makarantun firamare da na ƙananan yara, yayin da a sakandiren ƙasa adadin ya kai 122 ga bayan gida guda, sannan a sakandiren gaba da sakandire ya kai 73.
Binciken ya shafi dukkan makarantun firamare da na ƙananan yara 7,331, makarantun sakandiren ƙasa 1,451, sakandiren gaba da sakandire 800, makarantun kimiyya da fasaha 49 da cibiyoyin ilimin manya 63 a faɗin jihar. Sai dai duk da waɗannan matsaloli, rahoton ya nuna ci gaba mai kyau wajen yawan shiga makaranta, musamman a tsakanin ‘yan mata.
’Yan mata sun kai kashi 52 cikin 100 na masu rajista a makarantun firamare da na ƙananan yara, kashi 56 cikin 100 a sakandiren ƙasa, sannan kashi 54 cikin 100 a sakandiren gaba da sakandire.
A matakin firamare kaɗai, adadin ɗalibai ya kai 4,034,744, ciki har da ‘yan mata 2,095,761. A sakandiren ƙasa kuma an samu ɗalibai 509,314, inda 284,708 daga cikinsu mata ne.
Rahoton ya kuma nuna cewa malamai 45,007 ne ke aiki a tsarin ilimin gwamnati na Kano, mafi yawansu kuma suna koyarwa ne a matakan firamare da na ƙananan yara.
ƙidayar Makarantu Ta Shekara wata muhimmiyar hanya ce da gwamnati da abokan hulɗarta na ci gaba ke amfani da ita wajen tantance yawan ɗalibai, buƙatun gine-gine da giɓin kayan aiki a fannin ilimi.
Wannan sabon rahoto ya zo ne kusan shekaru biyu bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimi saboda lalacewar makarantu da ƙaruwar yaran da ba sa zuwa makaranta.
Yayin wata liyafa a Fadar Gwamnatin Kano a lokacin, gwamnan ya bayyana cewa matakin ya zama wajibi domin magance durƙushewar ingancin ilimi da kayan ci gaban karatu. Ya ce dokar ta-ɓacin wata dama ce ta ɗaukar matakai masu ƙarfi da gaggawa domin gyara matsalolin da suka addabi fannin. Gwamnan ya kuma bayyana cewa a lokacin akwai yara 989,234 da ba sa zuwa makaranta a Kano, yana mai gargadin cewa hakan na barazana ga makomar gaba ɗaya.
Ya ce makarantu da dama sun lalace ƙwarai, inda rufuffuka ke faɗowa, bango na rushewa, kuma azuzuwa ba sa samar da yanayin karatu mai kyau. A cewarsa, sama da yara miliyan 4.7 ne ke zama a ƙasa suna karatu, yayin da kusan makarantu 400 ke da malami guda da ke koyar da dukkan azuzuwa da darussa.
A matsayin wani ɓangare na matakan gaggawa, gwamnan ya amince da ɗaukar ƙarin malamai 10,000 tare da shirye-shiryen horaswa da sake horas da malamai. Haka kuma ya amince da ɗaukar ma’aikatan koyarwa da waɗanda ba na koyarwa ba su 1,000 a manyan cibiyoyin ilimi. Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta biya kuɗin rajistar ɗaliban Kano da ke manyan makarantu a faɗin ƙasar nan.
A wancan lokacin, Kwamishinan Ilimi, Alhaji Umar Doguwa, ya sanar da cewa gwamnan ya amince da biyan kuɗin jarrabawar NECO da NBAIS ga sama da ɗalibai 118,000 ‘yan asalin Kano.
A halin yanzu, Kwamishinan Ilimi na jihar, Ali Haruna Makoɗa, ya amince da cewa har yanzu akwai manyan ƙalubale, amma ya jaddada cewa gwamnati na ci gaba da aiwatar da manyan ayyuka domin gyara ɓarnar da aka gada.
Yayin wata ziyara da ƙaramin Ministan Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ta kai Kano domin duba ayyukan shirin AGILE, Makoda ya bayyana cewa an bayar da kwangilolin sama da naira biliyan 24 domin gina sabbin makarantu 49. Ya kuma ce ana shirin gyaran makarantu 300 a dukkan unguwanni 484 na jihar. A cewarsa, ilimi ne ke ci gaba da samun kaso mafi girma na kasafin kuɗin jihar, inda aka ware masa kashi 29.75 cikin 100 a 2024, kashi 31.5 cikin 100 a 2025, da kuma kashi 30 cikin 100 a 2026.
Makoɗa ya bayyana cewa an gyara sama da azuzuwa 2,500 tare da ɗaukar malamai sama da 18,000 domin rage gibin ma’aikata a makarantu. Ya ƙara da cewa, sabuwar manufar tura malamai aiki ta tanadi cewa sabbin malamai za su yi aiki a yankunansu domin tabbatar da cewa karkara ba ta koma baya ba.
Sai dai duk da waɗannan matakai, sabon rahoton ƙidayar Makarantu Ta Shekara ya nuna cewa cunkoson azuzuwa, ƙarancin malamai da kuma ƙarancin kayayyakin more ilimi na ci gaba da kasancewa manyan ƙalubalen da ke gaban tsarin ilimin gwamnati a Kano.
