Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kare Haƙƙin Masu Saye ta Tarayya (FCCPC) ta yi gargaɗi ga dillalan man fetur a ɓangaren rarrabawa da sayarwa da su daina anfani da buƙatuwar mutane ta hanyar ƙin rage farashin fetur duk da faɗuwar da aka samu a farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.
Mataimakin Shugaban Hukumar kuma Babban Darakta na FCCPC, Tunji Bello, ya bayyana damuwa kan yadda binciken da hukumar ke ci gaba da yi a kasuwar man fetur ya nuna cewa matatun mai na cikin gida, masu kasuwancin man fetur, masu tankunan ajiyar mai da gidajen sayar da mai sun rage farashin mai kaɗan ne kawai, duk da gagarumar saukar da aka samu a farashin ɗanyen mai a duniya.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Ondaje Ijagwu, ya fitar, Bello ya jaddada cewa duk da cewa FCCPC ba ita ce ke ƙayyade ko amincewa da farashin man fetur a kasuwar da aka yi wa sassauci ba, hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen bincike da hukunta duk wani kamfani da aka samu da laifin cin zarafin mabuƙata, yaudararsu ko kuma aikata abubuwan da suka saɓa wa Dokar Kare Gasa da Haƙƙin Masu Saye ta Tarayya ta shekarar 2018.
“Domin a fayyace, hukumar ba ta ƙayyade ko amincewa da farashin man fetur a kasuwar da aka yi wa sassauci. Aikinmu a ƙarƙashin Dokar FCCPA ta 2018 shi ne tabbatar da gasa mai adalci a kasuwa, hana ayyukan da ke kawo cikas ga gasa, da kuma kare mabuƙata daga duk wata mu’amala ta rashin adalci, yaudara ko cin zarafi,” inji Bello.
Ya ƙara da cewa, hukumar na mamakin yadda dillalan man fetur ke saurin ƙara farashi idan farashin ɗanyen mai ya tashi, amma idan ya sauka sai a ɗauki lokaci mai tsawo kafin mabuƙata su amfana da raguwar.
“Muna ganin cewa kasuwa mai gasa ta gaskiya ya kamata ta yi aiki ta hanyar da za ta amfani mabuƙata a kowane hali, ko lokacin tashin farashi ko lokacin saukarsa,” ya ce.
Shugaban FCCPC ya bayyana cewa farashin ɗanyen mai a duniya ya ragu sosai zuwa kusan dala 73 kan kowace ganga bayan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran da kuma sake buɗe mashigar Hormuz, idan aka kwatanta da kusan dala 120 da ganga ta kai a watan Afrilu lokacin da rikicin yankin Tekun Fasha ya yi ƙamari.
Hukumar ta lura cewa duk da dawowar farashin ɗanyen mai zuwa matakin da yake a watan Fabrairu, har yanzu ba a ga raguwar da ta dace ba a farashin man fetur a cikin gida.
Ta tunatar da cewa lokacin da farashin ɗanyen mai ya tashi a baya, matatun mai da dillalai sun yi gaggawar ƙara farashin fetur zuwa tsakanin naira 1,350 da 1,500 kan lita, yayin da dizal ya kai kusan naira 2,000 kan lita.
A watan Fabrairu kuwa, ana sayar da fetur tsakanin naira 800 zuwa 900 kan kowace lita. Sai dai duk da raguwar farashin ɗanyen mai a duniya, FCCPC ta ce har yanzu ana sayar da fetur a matsakaicin farashin kusan naira 1,200 kan lita a faɗin ƙasar nan, yayin da wasu matatun mai na cikin gida ke sayarwa ga dillalai tsakanin naira 1,025 da 1,075 kan lita.
Rahoton ya nuna cewa a lokacin haɗa wannan labari, farashin ɗanyen mai na Brent a kasuwar duniya ya tsaya a dala 72.44 kan ganga, ƙasa da sama da dala 100 da ya kai kafin ɓarkewar rikicin.
Bello ya amince cewa farashin man fetur a cikin gida yana dogara ne da wasu abubuwa da suka haɗa da kuɗin tace mai, canjin kuɗaɗen ƙasashen waje, sufuri, kuɗin rance da rarrabawa. Sai dai ya ce da a ce ana gudanar da kasuwa cikin adalci, da mabuƙata sun fara amfana da raguwar farashin cikin sauri.
Ya jaddada cewa sassauta kasuwa ba ya kawar da alhakin kamfanoni na yin gasa cikin adalci ko kuma haƙƙin mabukata na samun farashi mai kyau.
“Idan muka samu sahihan hujjojin da ke nuna cewa wani kamfani na aikata abin da ke kawo cikas ga gasa, cin zarafin mabuƙata ko karya dokar FCCPA, hukumar za ta gudanar da bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace,” inji Bello.
Ya kuma buƙaci ’yan Nijeriya da su riƙa kai rahoton duk wata alamar rashin gasa ta gaskiya, farashi mai ruɗani ko wasu halayen kasuwanci marasa adalci ta hanyoyin karɓar ƙorafe-ƙorafen da hukumar ta tanada.
A cewarsa, FCCPC za ta bai wa duk wata ƙorafi mai inganci kulawar da ta dace domin kare haƙƙin mabuƙata.
